Shugaban kasar Iran ya koma Tehran bayan halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai
Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya dawo Tehran daga Bishkek, babban birnin Kyrgyzstan, bayan halartar taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) da kuma taron Shanghai Plus, sannan ya gana da shugabannin kasashen da suka halarci taron.
A lokacin ziyarar kwanaki biyu da ya kai Kyrgyzstan, Shugaba Pezeshkian ya yi jawabi a taron kolin SCO da kuma taron Shanghai Plus, inda ya bayyana matsayin Jamhuriyar Musulunci kan batutuwan yanki da na duniya.
Shugaba Pezeshkian ya kuma gana da shugabannin kasashen China, Rasha, Tajikistan, Azerbaijan, da Kyrgyzstan, da kuma fira ministocin Indiya da Pakistan, domin tattauna dangantakar kasashen biyu da muhimman batutuwan yanki da na duniya.
A lokacin ziyarar tasa, Shugaba Pezeshkian ya kuma gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres.