Rahotanni da suke fitowa daga yankin ‘Sahalul-Khayam na kasar Lebanon sun ce, wasu ‘yan asalin kasar Syria su 2 sun yi shahada sanadiyyar harin da Isra’ila ta kai da jirgin sama maras matuki sa’o’i 2 da su ka wuce.
Da safiyar yau Litinin ma dai wani karamin jirigin ‘yan sahayoniya ya jefa bom akan wata mota da take tafiya a garin “Beit-Lif” a kudancin kasar da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar wanda ke cikinta.
Hare-haren da HKI take kai wa a kudancin Lebanon din dai yana a karkashin keta hurumin kasar da kuma kin aiki da kudurin MDD mai lamba 1701 na tsagaita wutar yakin da aka yi a ranar 27 ga watan Nuwamba na shekara 2024.