Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Lokaci ya yi da za a amince da takunkumin da bai dace ba a matsayin laifi ga bil’adama
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce lokaci ya yi da za a amince da takunkumin bai daya da Amurka da kawayenta suka kakaba wa Iran a matsayin wani laifi na cin zarafin bil adama.
A cikin shafinsa na dandalin X, Araqchi ya bayyana cewa: “Gwamnatocin yammacin duniya a koyaushe suna da’awar cewa takunkumin zaman lafiya ne maimakon yakin zubar da jinni, amma gaskiyar tana bayyana wani labari na daban.”
Ya yi nuni da wani bincike na baya-bayan nan da aka buga a cikin jaridar The Lancet, wanda ya nuna cewa takunkumin bai-daya-musamman wanda Amurka ta kakabawa—na iya zama mai kisa kamar tashe-tashen hankula.
Ya kara da cewa; “Tun daga shekara ta 1970, sama da mutane 500,000 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon takunkumin da aka sanya musu, inda akasarin wadanda abin ya shafa yara ne da kuma tsofaffi.”