Miliyoyin musulmi daga ko ina sun taru a hubbaren Imam Hussain (a) da ke birnin Karbaka na kudancin kasar Iraki, don girmama limami na 3 daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) wanda ya zama a bin buga misali a duk tsawon tarihin musulunci na nuna turjiya da kuma fada da azzalumai.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Iran ta bayyana cewa miliyoyin musul daga cikin kasar Iraki da kuma wajensa ne suke tattaki da kafa daga ko ko ta ina a cikin kasar zuwa hubbaren Imam Hussain (a). Sannan a kan hanyarsu ta zuwa Karbala akwai dubban mutane masu sa kai, suna raba ruwa da abinci da samarda wuraren hutawa da kuma magani ga wadanda suke bukata. Inda suke neman al-barkan Imam Hussain (a) da masu ziyararsa.
Imam Husain(a), a ranar ashoora ko 10 ga watan muharram na shekara ta 61 bayan hijira ko kuma 680 miladiyya tare da magoya bayansa 72 suka fuskanci rundunar azzalumin sarki na lokacin Yazid dan Mu’wiya wadanda suka kai akalla dubu 30,000. Ba tare da wani tsoro ba suka fuskanci makiyan har zuwa karshensu.
Da wannan kuma da shi da sahabbansa suka zama abin buga misali na jarunta da kuma fada da zalunci, a duniya, sannan a yanzun da kuma nan gaba sun zasu ci gaba da zama abin tsoro ga azzalumai har duniya ta dane.
Labarin ya kara da cewa daga kasar Iran kadai iraniyawa 5,291,005 ne suka tsallaka kan iyakar kasashen biyu daga kofofin 6 don halattar juyayin 40 na Imam Hussain (a) na bana a Karabala.
Sannan a cikin gida kuma an gudanar da juyayin a garuruwa kimani 500. A nan Tehran an gudanar da tattaki daga dandalin Imam Hussain (a) zuwa Haramin sha Abdulazim alhassani da ke garin Rey wajen birnin Tehran.