Miliyoyin Mutane Sun Taru A Karbala Don Juyayin 40 Na Shahadarsa Imam Hussain(a)

Miliyoyin musulmi daga ko ina sun taru a hubbaren Imam Hussain (a) da ke birnin Karbaka na kudancin kasar Iraki, don girmama limami na 3 daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) wanda ya zama a bin buga misali a duk tsawon tarihin musulunci na nuna turjiya da kuma fada da azzalumai. Tashar […]
Sayyid Huthi Ya Yi gargadi Yiyuwar Tarwatsewar kasashen yankin idan HKI Ta Tabbaga Shirinta

Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyeed Abdulmalik Badruddeen Huthi , a jawabinsa na mako-mako da ya saba gabatarwa, dangane da Falasdinu da kuma sabbin al-amura da suka faru ko suke faruwa a yankin da kuma duniya gaba daya ya tabo al-amura da dama. Tashar talabijin ta Al-Alam wacce take watsa shirye shiryenta da harshen […]
An Bukaci Ficewar Marasa Lafiya da Likitoci daga Wani Babban Asbiti A birnin London

Jami’an kwana-kwana a birnin London na kasar Burtaniya sun bukaci marasa lafiya da likitoci da sauran masu aikin a asbitin Guy da su fice daga asbitin saboda hatsarin samuwar wasu sinadarai masu cutarwa a cikinsa. Jaridar da Nation ta kasar Amurka ta bayyana cewa , da masalin karfe 8.49 ne aka shaidawa jami’an kwana-kwana batun […]
Za’a Fara tattaunawar Kasa Dangane Da Talauci da Rashin Adalci A Rabon Arziki A Afirka da Kudu

Gwamnatin kasar Afirka ta kudu zata fara tattaunawar kasa dangane da talauci da kuma rashin adalci a rabon arziki a kasar. Gwamnatin kasar ta ware kimani dalar Amurka miliyon 40$ don gudanar da tattaunawar. Inda ake saran dukkan mutanen Afrika ta kudu suna da damar bayyana ra’ayinsu dangane da wadannan matsaloli. Na talauci da rashin […]
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi tsokaci kan furucin Netanyahu game da kafa ‘Babban Kasar Isra’ila’ Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana a safiyar yau alhamis cewa: Kafafen yada labaran yammacin duniya a al’ada na zargin duk wanda ya ambaci ra’ayin ‘yan sahayoniyya na kafa “Babban kasar Isra’ila” da kiyayya ga wata […]
Iran Ta Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashen Yankin

Kasar Iran ta jaddada wajabcin daukar kwararan matakai na kasa da kasa don dakile muradun gwamnatin mamaya na mulkin mallaka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya yi Allah wadai da kalaman fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ake nema ruwa a jallo a kotun kasa da kasa ya yi dangane da abin da […]
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Isra’ila A Matsayar ‘Yar Yaudara

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya Bayyana cewa: Shugabannin gwamnatin nuna wariyar al’umma suna kokarin yaudarar al’ummar Iran A martaninsa ga fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ya yi a baya-bayan nan, shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Kasar Iran a yayin da yake gabatar da wasu takardu kan matsalar karancin ruwa da kuma matsalar […]
Hizbullahi Ta Yaba Wa Iran Kan Irin Gudumawarta Ga Lebanon Da Gwagwarmaya

Babban sakataren kungiya Hizbullahi ta kasar Lebanon ya karbi bakwancin Ali Larijani ya kuma godewa Iran bisa goyon bayan da take baiwa kasar Lebanon da ‘yan gwagwarmaya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassem ya gana da Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran da […]
Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Fatali Da Batun Kafa Gwamnatin Hadaka A Kasar Sudan

Gwamanatin Sudan ta yi maraba da sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na yin Allah wadai da shirin kafa gwamnatin hadaka a kasar Sudan Sudan ta yi marhabin da sanarwar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a jiya Laraba, inda ta yi watsi da shirin dakarun kai daukin gaggawa na kafa […]
Larijani a Beirut: Iran A Shirye take ta taimaka ma Lebanon

Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri ya tarbi Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran a hedikwatar shugaban kasa ta biyu dake Ain al-Tineh. Larijani ya tabbatar da cewa bayan ganawar da aka yi tsakanin kasashen Labanon da Iran lamarin ya yi kyau da armashi. Ya jaddada cewa Iran ba ta da […]
Masar ta yi Allawadai da furucin Netanyahu kan shirin kafa Isra’ila Babba

Masar ta yi Allawadai da kalaman Benjamin Netanyahu game da abin da ya kira shirinsa na kafa babbar kasar yahudawa ko kuma Isra’ila Babba. Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, bayan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana kan wanann batu, wanda ya tayar […]
Hamas ta aike da sakon jinjina ga al’ummar Yemen kan goyon bayan Gaza

Ministan harkokin wajen Yemen Jamal Amer a ranar Laraba ya karbi wata wasika daga Dr. Khalil al-Hayya shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda wakilin kungiyar a Sanaa, Moaz Abu Shamala ya mika. A cikin wasiƙar nasa, al-Hayya ya bayyana matuƙar godiyar Hamas ga sadaukarwa da tsayin dakan al’ummar Yemen, yana mai bayyana su a matsayin […]