MDD:Isra’ila Na Ci Gaba Da Yin Kisan Kare Dangi A Gaza

halin da alummar gaza ke ciki ya yi muni sosai saboda ci ga da kai hari da isra'ila ke yi

Wasu Kwararru na Majallisar dinkin duniya sun yi gargadin cewa isra’ila na ci gaba da yin kisan kare dangin kan alummar gaza duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan oktoba tsakaninsu da kungiyar Hamas, da ake sa ran zai kawo karshen hare-hare kan alummar falasdinu

A cikin wani bayani da suka wallafa a jiya litinin kwararrun na majalisar dinkin duniya sun nuna cewa fiye da falasdinawa 1200 ne aka kashe a yankin gaza daga lokacin da ka sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suka hada da wasu 160 a watan yuli.

Kwararrun sun yi gargadin cewa kisan kare dangi da isra’ila ke yi na ci gaba da gudana ba tare da tsayawa ba, kuma isra’ila ta hana isa ga filaye da gonaki da ma ruwan sha da sauran kayayyakin amfani gona, kuma yanzu haka isra’ila ta fadada kai hare-harenta kan falasdinawa a sauran yankuna da suka hada da gabar yammacin kogin jodan

Haka zalika sun yi ishara game da yadda isra’ila take kara fadada gine gine fiye da kowanne lokaci a yankunan falasdinawa  da kuma rusa gidaje da kwace filaye da kuma rufe sansanonin yan gudun hijira na tsawon lokacin da yake samun goyon bayan mukarabban gwamnatin isra’ila da kara musu karfin guiwa a gabar yammacin kogin jodan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted