Search
Close this search box.

Masar Za Ta Shiga Shari’ar Da Afirka Ta Kudu Ta Shigar Kan Isra’ila A Kotun ICJ

Kasar Masar ta bayyana a ranar Lahadi cewa za ta shiga shari’ar kisan kare dangi da Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra’ila a kotun

Kasar Masar ta bayyana a ranar Lahadi cewa za ta shiga shari’ar kisan kare dangi da Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra’ila a kotun kasa da kasa ta ICJ.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar, ta ce wannan matakin na zuwa ne “a bisa la’akari da tsananantar hare-haren da Isra’ila ke kai wa kan fararen hula Falasdinawa a Gaza da kuma kai hari kan fararen hula da lalata ababen more rayuwa a cikin tsibirin.”

Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Masar ta zo ne a daidai lokacin da sojojin Isra’ila ke ci gaba da dannawa a kan iyakar Masar da zirin Gaza, matakin da Alkahira ta ce zai iya kawo cikas ga yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

Sanarwar ta ce, matakin ya zo ne bisa la’akari da muni da kuma girman hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kan fararen hula a zirin Gaza, da kuma ci gaba da kai hare-hare kan al’ummar Palasdinu, da lalata ababen more rayuwa a yankin, lamarin dake tilastawa Falasdinawa su gudu.”

Masar ta ce ba za ta bude iyakokinta ba domin baiwa dimbin mazauna Gaza damar tserewa fadan. Har ila yau, ta rufe hanyar mashigar Rafah don nuna adawa da matakin sojojin Isra’ila.

Sanarwar ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba don tsagaita bude wuta a Gaza da kuma kawo karshen ayyukan sojin Isra’ila a Rafah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments