Masar Za Ta Bayyana Shirin Sake Gina Gaza A Yayin Taron Larabawa

Babban jami’in diplomasiyyar kasar Masar ya sanar da cewa; Shirin da kasarsa take da shi na sake gina Gaza, abu ne mai yiyuwa a aikace,

Babban jami’in diplomasiyyar kasar Masar ya sanar da cewa; Shirin da kasarsa take da shi na sake gina Gaza, abu ne mai yiyuwa a aikace, kuma za a aiwatar da shi ba tare da an kori mutanen Gaza ba.

Badr Abdul’adhy,  ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da fira ministan gwmanatin kwarya-kwaryar Falasdinu gabanin yin taron kasashen larabawa a birnin alkahira.

Ministan harkokin wajen kasar ta Masar ya ce; “Hanya daya tilo ta kawo karshen yawan fadace-fadace, shi ne a  cusa wa Falasdinawa fatan jin cewa,abinda suke mafarki da shi mai yiyuwa ne a aikace,wanda shi ne kafa ‘yantacciyar kasarsu.”

Haka nan kuma ya ce; Shirin da Masar take da shi na sake gina Gaza, mai yiyuwa ne a aikace, kuma cikin wani matsakaicin zango na lokaci, bai kuma bukatar a ce sai mutane sun bar kasarsu.”

 Wannan shirin na Masar dai ya zo ne bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya  ce za a kori Falasdinawa su miliyan biyu daga Gaza saboda sake ginata da kuma yin wasu manyan gine-gine na kasuwanci.

Kalaman na shugaban kasar Amurka sun fuskanci mayar da martani mai tsanani daga Falasdinawa, kasashen Larabawa, da kuma  wasu kasashen turai.

A nashi gefen, Fira ministan Falasdinu Muhammad Mustafa ya bayyana fatansa na samun cikakken goyon bayan kasashen larabawa domin aiwatar da shirin na kasar Masar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments