Masana Fasahar Gina Jiragen Sama A Iran Sun Samar Da Wata Fasahar Nano Mai Rage Nauyin Jiragen Sama

Masu fasahar gina jiragen sama a kasar Iran sun samar da wani sinadari wanda ake kira ‘Smart Magnesium’ wanda ake iya rage nauyin jiragin sama

Masu fasahar gina jiragen sama a kasar Iran sun samar da wani sinadari wanda ake kira ‘Smart Magnesium’ wanda ake iya rage nauyin jiragin sama da shi.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu binciken na cewa sun samar da wani sinadari wanda baya sanya ‘magnesium Alloy’ a jikin jiragen sama tsatsa, kuma idan an rufe jikin jirgi da shi zai rage nauyinsa. Banda haka zai kyautata yanda jirage zasu sarrafa makamashin jirgin.

Rahoton ya kara da cewa wannan kirkirar ya na da muhimmanci a kamfanonin kera jiragen sama, da kuma samar da  injuna, saboda zai kara dadewar jikin jiragen sama, kafin yayi tsatsa. Har’ila yau ya kuma taimaka wajen rage nauyin jikin jirgin.

Banda haka sabon fasahar da aka gano dai, zata tsawon lokacin amfani da jikin  fiye da yadda yake a yanzun. Labarin ya kammala da cewa Wannan fasahar zai taimakawa jiragen sama da kuma kumbo masu zuwa sararin samaniya.

Roqaieh Samadian-Fard, kwararre a wannan fannin ya bayyana cewa kafin haka ana samun matsalar tsatsar jikin jiragen sama da sauri, idan an kwatanda da wannan sabon sinadarin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments