Search
Close this search box.

Manyan Hafsoshin Tsaron ECOWAS Na Taro A Abuja

Manyan hafsoshin tsaron kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) sun fara taro a Abuja, babban birnin Najeriya a safiyar Laraba. Ministan Tsaron Najeriya, Muhammad Badaru da takwaransa

Manyan hafsoshin tsaron kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) sun fara taro a Abuja, babban birnin Najeriya a safiyar Laraba.

Ministan Tsaron Najeriya, Muhammad Badaru da takwaransa na Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, da Mashawarcin Shugaban Kasa kan sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu, sun hallara a zauren taron.

Kazalika daukacin Manyan hafsoshin tsaron kasashen ECOWAS sun hallara, in banda na kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, wadanda suka ce sun fice daga kungiyar.

Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, da takwaransa na Majalisar Wakila na cikin mahalarta taron.

Mai masaukin baki, Shugaban Kwamitin Manyan hafsoshin ECOWAS kuma Babban Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christoper Musa, yana jagorantar taron ne a daidai lokacin da hukumomin tsaron kasarsa ke neman murkushe tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar gama-gari kan tsadar rayuwa a fadin kasar.

Bisa umarnin Shugaba Kasa, Bola Ahmed Tinubu, hukumomin tsaron Najeriya na kokarin dakile abin da suka kira barazanar tsaro da cin amanar kasa, bayan da masu zanga-zangar suka rika daga tutocin kasar Rasha da kuma neman mulki ya koma hannun sojoji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments