Mali: Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Mahakar Ma’adinai A Kudancin Kasar

Yan bindiga a kasar Mali sun kai hare-hare kan mahakar ma’adinai daga kudancin kasar a karshen makon da ya gabata inda suka kona kayakin aikin

Yan bindiga a kasar Mali sun kai hare-hare kan mahakar ma’adinai daga kudancin kasar a karshen makon da ya gabata inda suka kona kayakin aikin hakar Ma’adinai, sannan suka yi garkuwa da mutane 7 na wani lokaci kafin su sake su daga baya.

Tashar talabijan ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto jami’an gwamnatin kasar Mali a ma’aikatar ma’adinai suna fadawa dan rahoton kamfanin dillancin labaran reuters kan cewa,  yan bindiga sun kai hare-hare kan mahakar ma’adinai ta Manjam Morila inda suka kona kayakin aikin hakar ma’adinan suka kuma kama mutane 7 a matsayin garkuwa amma bayan sun sami damar tserewa sun sakesu.

Labarin ya kasar da cewa kasar Mali ta dade tana fama da yan ta’adda wadanda suke aiki da kungiyar al-ka’ida, wadanda kuma suke kokarin wargaza tattalin arzikin kasar saboda taimakawa kasashen yamma wadanda ta kora daga kasar.

Kasar Mali dai ita ce kasa ta uku a nahiyar Afrika mai arzikin zinari. Kuma ba wannan ne karo na farko wanda wadan nan yan ta’adda suke kai hare-hare kan dukiyar gwamnatin kasar Mali don gurgunta rayuwar mutanen kasar ba. A cikin shekarar da ta gabata, yan ta’addan sun toshe hanyar da kasar take shigo da makamashi daga kasar Senegal ta kuma kona tankunan man fetur da gas wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa birnin bamako babban birnin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted