Jama’a masu dimbin yawa na tururuwa zuwa birnin Karbala mai tsarki daga Najaf domin halartar yuyayin ranar Arbaeen a cikin tsauraran matakan tsaro da na hidima.
Wakilin Al-Alam da ke kan titin Karbala Mo’ataz Al-Aboudi ya ruwaito cewa: Ana ci gaba da zirga-zirgar masu ziyarar Arbaeen lami lafiya duk kuwa da tsananin zafi a kan hanyoyin da ke kan hanyar zuwa Karbala.
Wakilin na Al-Alam ya bayyana cewa: Birnin Karbala mai tsarki yana sa ran halartar masu ziyara sama da miliyan 4 daga wajen kasar Iraki, a cewar gwamnan Karbala Jassim Al-Khattabi. Ya yi nuni da cewa adadin masu halartar taron na iya zarce wannan adadin, domin mashigar kan iyaka da filayen tashi da saukar jiragen sama na ganin dimbin masu ziyara da ke shiga Iraki.
Wakilin Al-Alam ya bayyana cewa: Filin jirgin saman Najaf ya sanar da karbar jirage sama da 150 daga sassa daban-daban na duniya dauke da masu ziyarar Imam Husaini {a.s}.