Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Wannan Talata

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a gobe talata mataimakin shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya zai ziyarci kasar, amma ba tare da zuwa cibiyoyin nukliya na kasar ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne ziyarar aiki na farko wanda wani jami’in hukumar ya […]
Iran: Lebanon Tana Da ‘Yancin Kare Kanta Da Makamanta

Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa kasar Lebanon tana da hakkin kare kanta, kuma tana bukatar makaman kungiyar hizbullah don yin haka. Kumfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Bakae yana fadar haka a yau litinin ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Iran ta yi imanin […]
Mali: An Kama Sojoji Fiye da 40 Bisa Zargin Yunkurin Juyin Mulki

Sojojin Kasar Mali kimani 45 aka kama biyu daga cikinsu masu mukamin Janar a karshen makon da ya gabata a kokarin da suka yi na juyin mulki a kasar Shafin yanar gizo na labarai ;Afrika News: ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka kama har da janar Abass Dembele, kuma tsohon gwamna na lardin Tsakiyar […]
Iraki: Larijani Da Sudani Sun Gana A Bagdaza

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, Dr Ali Larijani ya gana da firai ministan kasar Iraki Mohammad Shia Assudani a birnin bagdaza inda bangarorin biyu suka tattauna al-amura da dama da suka shafi harkokin tsaro a tsakanin kasashen biyu da kuma matsalolin yankin wadanda suka hada da kasar falasdinu. Kamfanin dillancin labaran Tasnim […]
Mafi yawan Kasashen Duniya Sun Amince Da Samarda Kasar Falasdinu

Kashi 3/4 na kasashe mambobi a majalisar dinkin duniya sun amince da samar da kasar Falasdinu, mai zaman kanta tare da kasar Australia a yau Litinin ta bada sanarwan cewa zata shelanta amincewarta da kasar Falasdinu a matsayin mai zaman kanta a taron babban zauren mdd wana za;a gudanar a cikin watan Satumba mai zuwa. […]
Mahukuntan Iraki: Adadin Masu Ziyarar Arba’een Daga Kasashen Ketare Zai Iya Haura Miliyan 40

Birnin Karbala mai tsarki na sa ran karbar bakwancin masu ziyara sama da miliyan 4 daga kasashen ketare domin gudanar da juyayin Arbaeen Jama’a masu dimbin yawa na tururuwa zuwa birnin Karbala mai tsarki daga Najaf domin halartar yuyayin ranar Arbaeen a cikin tsauraran matakan tsaro da na hidima. Wakilin Al-Alam da ke kan titin […]
Sojojin Mamayar Isra’ila Sun kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Yankunan Zirin Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila sun harba wata mugunyar ‘karfin wuta’ da jiragen saman yaki kan yankin kudancin Gaza Bayan tsakar dare ne jiragen yakin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar da luguden wuta a kudancin birnin Gaza. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta nakalto majiyoyin da ta bayyana a matsayin na cikin gida na cewa: Jiragen saman […]
Kwamitin Tsaron MDD Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar Isra’ila A Kan Gaza

Kasashen Turai biyar na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da matakin mamaye Gaza Wakilin dindindin na Slovenia ya gabatar da wata sanarwa ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a madadin Burtaniya, Faransa, Denmark, da Girka, yana mai cewa: “A matsayinsu na kasashen Birtaniya, Denmark, Faransa, Girka, da Slovenia, sun kira taron gaggawa […]
Shugaban Iran: Dole ne duniya ta kawo karshen laifukan yakin Isra’ila a Gaza

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce dole ne dukkan kasashen duniya su yi kokarin kawo karshen laifukan da Isra’ila ke aikatawa a zirin Gaza da kuma kawo karshen killacewa da take yi wa yankin. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake karbar takardar shaidar sabbin jakadun kasashen […]
Israila Ta Kashe ‘Yan Jarida 4 A Harin Da Ta Kai Kan Tantinsu A Gaza

‘Yan jarida 4 Anas al-Sharif da Mohammad Qraiqea, da masu daukar hoto Mohammad Nawfal da Ibrahim Daher sun shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai kan wani tantin ‘yan jarida a arewacin zirin Gaza. Anas al-Sharif, shahharen dan jarida wanda ya sha bayar da rahotonnai da suke fallasa ayyukan kisan kare dangi […]
Iran: Ba a yanke wani abu game da tattaunawa da Washington ba

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa “babu wani abu da aka yanke ya yanzu game da tattaunawa da Amurka,” ya kara da cewa “babu wani tabbci kan zabar wata kasa da za ta karbi bakuncin tattaunawar.” A jawabin da ya yi a gefen taron majalisar ministocin a jiya Lahadi, Araqchi ya […]
Kwamitin Tsaro ya yi zaman gaggawa kan Shirin Isra’ila na mamaye Gaza

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da majalisar ministocin Isra’ila ta dauka na fadada ayyukan soji da kuma mamaye yankin zirin Gaza. Mataimakiyar Sakatare-Janar mai kula da harkokin Turai, Tsakiyar Asiya da Amurka, Miroslav Jenča, ta jaddada […]
Iraki: An bankado wani yunkurin kai wa masu ziyarar Arbaeen hari

Jami’an tsaron kasar Iraki sun sanar da gano wata kungiyar ‘yan ta’adda da ta yi niyyar kai wa masu ziyarar Arbaeen hare-hare, wanda aka shirya gudanarwa a kwanaki masu zuwa. Ma’aikatar tsaron ta bayyana cewa, “tsarin da ‘yan ta’addan ke da shi sun hada da dasa ababen fashewa a kan hanyoyin da masu tattaki ke […]