Kwance Damarar Dakarun Hashdu Zai Ragewa Harkokin Tsaron Kasar Iraki Aminci

Babban sakataren dakarun Asa’ibu Ahlul Hakki na kasar Iraki ya karyata zancen cewa za’a kwance damarar dakarun Hashdu sha’abi na kasar ta Iraki Kamfanin dillancin

Babban sakataren dakarun Asa’ibu Ahlul Hakki na kasar Iraki ya karyata zancen cewa za’a kwance damarar dakarun Hashdu sha’abi na kasar ta Iraki

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Qais Al-Khaz’ali ya na karyata wannan labarin, ya kuma bayyana haka ne a wani shiri a tashar talabijin ta Al-Irakiyya na kasar ta Iraki a jiya Lahadi.

Al-Khaz’ali ya kara da cewa makaman da suke karkashin kula na Hashdu sha’abi suna karkashin kula mai kyau, don haka babu tsaron cewa za’a yi amfani da su a inda bai dace ba. Ya kuma kara da cewa, tsarin tsaro na kasar ta Iraki yana da matukar muhimmanci garemu. Sannan ya kammala da cewa kwance damarar dakarun Hashdu Ashabi zagon kasa ne ga tsaron kasar ta Iraki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments