Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa Hamas da Jihadul-Islami sun yaba da martanin da Iran ta mayar kan laifuka da keta dokokin ‘yan mamaya
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta yaba da martanin da Iran da Yemen suka mayar kan Haramtacciyar kasar Isra’ila kan laifukan da take yi wa Lebanon da mutanenta, tana mai jaddada cewa: Mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan Isra’ila sakamakon wuce gona da iri da takeyi kan al’ummar Falasdinawa a Gaza, Yammacin Kogin Jordan, da kuma Kudus, da kuma kan al’ummar Lebanon, ya zama muhimmin abu da ba za a iya jinkirtawa ba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, Kungiyar Hamas ta kara da cewa: Hare-haren wuce gona da irin Isra’ila yana buƙatar haɗin kai daga ɓangarori daban-daban a yankin da kuma duniya don kawo ƙarshensu, kamar yadda ta bayyana a fili cewa Yahudawan Sahayoniyya da kuma hare-harenta marasa iyaka su ne tushen dukkan tashin hankali a yankin da kuma mummunan tasirinsu a fagen ƙasa da ƙasa.”
A nata bangaren kungiyar Jihadul- Islami ta yaba da hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai wa wuraren da suke cikin yankunan Falasdinawa da aka mamaye, tana mai cewa suna da muhimmanci wajen dakile hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kaiwa.