214-Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmi na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////…Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (s) dan Faah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata mun kammala kawo maku ziyarar Imam Al-Hassan (a) zuwa kasar Sham inda ya yi ta muhawarori da Mu’awiya da mutanensa, a wurare daban daban. Wadanda suka hada da Amru dan Asi, walid dan Uqba, Marwan dan Hakam, Utbatu dan Abusufyan, kanin Mu’awiya, Mughira dan Shuba, Abdullahi dan Zubair, da sauransu.
Sannan Imam Al-Hassan (a) ya tabbatarwa Mu’awiya dan Abusufyan da mutanensa kan cewa, babu kamar iyalan gidan Manzon All..(s) a cikin al-ummar musulmi a ilmi da halaye masu kyau da kuma hatta shugabanci, wanda suke tsammanin bai iya ba.
Da wannan dalilin ne Mu’awiya yake jin tsoron kada mutane su fahinceshi su yi masa tawaye, su bi Imam Al-Hassan(a). don haka a duk lokacinda ya ga cewa an fara jayayya ko husuma wanda ya shafi banu Hashin da kuma banu umayya yakan yi kokari ya kashe wutar jayayyar. Don yanda shi da kansa ya fada, ba zai taba manta da yanda Imam Ali (a) ya sami nasara a kansa da mutanen sham a yakin siffin ba, idan ba don kaidin da suka yi masa, na daga al-kur’ani mai girma ba. Da kuma abubuwan da suka biyo baya yakin Khawarijawa da kuma taron yanke hukunci na daumata jandle ba.
Don haka muna iya cewa, tafiyar Imam Al-Hassan (a) zuwa kasar Sham, ta fiye ce ta nunawa mutanen kasar Matsayin iyalan gidan Manzon All..(s) a cikin al-ummar musulmi, sannan a wani bangare kara tabbatar da hujja a kan mu’awiya da masu goyon bayansa cikin sahabban Manzon All..(s), wadanda sun zauna tare da Manzon All..(s) sun kuma san matsayin iyalan gidansa(s), amma kuma suka yi watsi da su, bayan wafatinsa. Suka wulakantasu suka maida su saniyar ware a cikin al-amuran tafiyar da al-umma a wasu lokutan sun yakesu don hanasu karban hakkinsu wanda aka kwace tun wafatin Manzon All..(s).
Sannan mun san cewa Imam Al-Hassan (a) ya dauki alkawula da dama, daga wajen Mu’awiya dan Abusufyan, sai kamar yanda muka fada a baya, a jawabinsa na farko a Kufa ya bayyana cewa, dukkan alkawulan da yayi wa Imam Al-Hassan (a) da sauran mutane yaudara ce don kaiwa ga shugabanci, don haka ba zai cika ko guda daga cikinsu ba.
Saboda haka ne wasu daga cikin shi’arsa (a) suke cewa, shi ma yayi watsi da alkawulan tunda mu’awiya yayi watsi da su, amma Imam (a) ya dage a kansu. Bai sabawa ko guda daga cikin al-kawulan da suka cimma da Mu’awiya ba.
Mafi yawan al-ummu idan sun yi sulhu a tsakaninsu, sukan kiyaye sharuddan sulhun don a zauna lafiya, wannan kuma a ko wani addini kuma a ko ina ne a duniya, sukan yi haka ne don a tabbatar da zaman lafiya, a cikin al-umma.
Addinin musulunci ya himmatu sosai da cika al-kawali da kuma kiyaye sharudda na sulhuntawa tsakanin al-ummu ko kuma daddaikun mutane.
A cikin suratul Isra aya ta 24 All..yana cewa, {Ku cika alkawali, lalle alkawali abin tambaya ne} isra, 24.
A wata aya yana cewa:
{Kuma idan suka nẽmi taimakonku a cikin addini, to taimako yã wajaba a kanku, fãce a kan mutãne waɗanda akwai wani alkwari a tsakãninku.} Amfal 72.
A cikin wadan nan ayoyi All..ya wajabtawa musulmi su taimakawa musulmi wadanda basu yi hijira ba, a cikin al-amuran da suka shafi imaninsu da addininsu. Sai ya toge da, mushrikai wadanda musulmi sun rika sun kulla yarjeniyar zaman lafiya da su.
A nan All..na kodaitar da musulmi su cika alkawalinsu da wadanda ba musulmi ba. Ina ga wadanda addini ya hada ku. A wani hadisin Manzon All..(s) yana cewa {Muminai suna kan sharuddansu} wato basa sabawa sharuddan da suka cimma da wani musulmi ne ko ba musulmi ba. A wani hadisin yana cewa {idan mumini ya yi alkawali zai cika al-kawalinsa}.
Sannan Amirulmuminina (a) yana fada a cikin takardan da ya rubutawa Malikul Ashtar, wanda ya aika zuwa kasar Masar a matsayin gwamnansa a can, bayan shahadar Mohammad dan Abubakar, {Idan ka kulla al-kawali da makiyinka, ko ya dora masa wani alkawali, ka sauke alkawalinda ka cika shi, sannan ka dauke alkawalin da aka dora maka da aminci, ka sanya kanka garkuwa don kare abinda ka bayar, lalle babu wani abu daga All..wanda mutane suka hadu a kansa, duk tare da rarrabansu, ko soye soyen zukatansu, ko kuma bambancin ra’ayinsu, kamar cika alkawula….
}.
Wannan shi ne matsayin addinin musulunci dangane da cika alkawali da kuma kiyaye sharudda tsakanin mutane, musulmi ko wadanda ba musulmi ba. Musulunci ya mada shi wajibi, ya kuma bukaci a cika alkawali, ko a cika sharudda. Ya haramta saba masa da rashin cika shi.
Bayan haka, mu kowa zuwa ga sulhun da Imam Al-Hassan (a) yayi da Mu’awiya dan Abusfyan, mu ga iyakar cika alkawalin Mu’awiya ga wannan alkawala da sharuddan sulhun. Mu ga kuma yadda shi Imam al-Hassan (a) ya cika bangarensa na alkawulan sulhun.
Idan mun fara da Imam Al-Hassan(a), zamu ga cewa ya cika dukkan al-kawula da sharuddan da ya daukawa Mu’awiya a sulhun, kuma wannan bai fi abu guda ba wanda kuma shi ne kada ya yake shi. Imam (a) ya cika alkawalin, tunda bai yake shi ba har zuwa shahadarsa bayan shekaru 10 da kulla shi.
Dangane da wannan da dama daga cikin mabiyansa, ko shi’ar iyalan gidan Manzon All..(s) kamar Adiy dan Hatam Atta’I, da Hijru dan Adiy duk sun bukaci Imam (a) ya yi watsi da alkawulan da ya daukawa Mu’awiya na rashin yakarsa, tunda shima ya sab awa al-kawulan da ya dauka, amma Imam yaki amincewa ya saba alkawalin.
Amma Mu’awiya dan Abusufyan, bai cika ko da daya daga cikin al-kawula da sharuddan da ya daukawa Imam Al-Hassan (a). wannan duk tare da rantsuwan da yayi da sunan All.. kan cewa zai cika alkawulan da ya dauka.
Amman yan kwanaki bayan wannan shan rantsuwa da yayi, ya hau kan mimbari a kufa ya fadawa mutane kan cewa, ba zai cikawa Imam Al-Hassan (a) ko da kuda daga cikin alkawulan da ya dauka ba.
Don haka tun lokacin ya assasa zagin Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) a kan mambarin musulmi, ya assasa zagi iyalan gidan Manzon All..(s) a kan mimbarorin musulmi.
Ya kashe sahabban Amirul muminina(a) ya kashe Hijru dan Adiy da mutanensa, ya tilastawa musulmi yin bai’a ga dansa Yazid sannan ya kashe Imam (a) da guba. Duk wannan sabawa alkawullan da ya daukawa Imam Al-Hassan (a) a sulhun ne.
Ga wasu daga cikin alkawulan da Mu’awiya dan Mu’awiya ya saba ya kuma kasa cika su wa Imam Al-Hassan (a).
01-Zagin Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a).
Ko way a san cewa, al-adar mutane ne, idan mutum ya mutu, ba’a ambatonsa sai da alkhairi, ba’a ambaton laifukansa, amma Mu’awiya ya sabawa hakan, dangane da Amirulmuminin(a). Mu’awiya ya sabawa wannan al-adar mutane, duk da cewa ya dauki alkawali kan rashin yin haka kafin sulhunsa da Imam Al-Hassan(a).
Wata kasida na cewa:
Girmama mamata wajibine -ko da ba dangimmu ba, ko ta yaya idan makusanta ne.
Mu’awiya ya maida zagin Imam Ali(a) da Ahlulbaitin Manzon All..(s) sunnan a cikin musulmi ta yanda barin haka laifi ne, wanda za’a azabtar da wanda yaki yin haka. Kai an kashe mutane da dama wadanda suka ki zagin Amirulmuminina (a). kamar yanda yayi da Hijr dan Adiy da mutanennsa. Wannan duk tare da cewa, an karbo hadisai sahihai daga Manzon All..(s) yana cewa: {Duk wanda ya zagi Ali ya zagi ne, wanda ya zage ni ya zagi All..} . A wani hadisan yana cewa {wanda ya cutar da Aliyu ya cutar da ni} Kamar yadda ya zo a cikin Musnad Ahmad.