Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 203

203-Assalamu alaikummasu sauraro barkammu a warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo

203-Assalamu alaikummasu sauraro barkammu a warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’asni mai girma, ko kumacikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha muttahari ko kuma cikin littafinMathnawi na mailana Jalaluddeen Rumi  ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///.. Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar ImamAl-Hassan Al-mujtaba(a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, mun tsaya a inda muka bayyana yadda wasu daga cikin mabiya Imam Al-Hassan (a) suka kadu suka kuma rikice bayan da labara ya zo masu kan cewa ya sulhunta da Mu’awiya dan Abu sufyan, ya kuma mika masa shugabancin Al-ummar Musulmi.

Mun kawo sunayen mutane da dama, daga ciki akwai Adi dan Hatam  Attaee, da Hijir dan Adiya, Musayyib dan Nujbah, da Bashir Alhamadani, da Sulaiman Dan Sard.

A yau zamu tashi daga Abdullahi dan Zubai, wanda dama yake da matsaloli tare da iyalan gidan manzon All..(s) a baya, inda ya yaki mahaifinsu Amirul mumina Aliyu dan Abutalib (a) tare da yafendosa Aisha ummul muminina a Basra, kuma ya taba yin khuduba yana zargin Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) da kissan Khalifa Usman a bainal Jama’a a Basra. Wanda kuma ba gaskiya bane, sai dai a lokacin yana son ingiza mutanen Basra su yaki amirul muminina (a) ne.

Don haka a lokacinda ya ji labarin sulhun da Imam Al-Hassan (a) yayi da Mu’awiya dan Abusufyan, sai ya shiga aibata shi, sai Imam (a) yace masa: Kana riya cewa na mika masa al-amari, kaitonka! ta yaya haka ya kasance? ina dan mafi jaruntar larabawa? Kuma Fatima shugaban matan aljanne ce ta haife ni? Kaitonka! Ban aikata haka ba, don tsoro ko rauni ba, sai dai mutane irinka ne suka yi mani bai’a, sannan suna son yanke ni, suna kuma nuna mani soyayye a zahiri, ni kuma ban amince da taimakon sub a.”.

Kafin haka Abdullahi dan Zubair, yana tuhumar Imam Al-Hassan (a) da tsoron yaki da mu’awiya (All..ya kiyeye shi, kamar yadda ya fada, daga ina ya gaji tsoro? Daga mahaifinsa wanda shi ne mafi jaruntar larabawa, zakin All..kuma zakin manzon All..(s) ? ko kuma daga kakanninsa manzon All..(s) da Abutalib(s), ko daga mahaifiyarsa diyar cikamakin annabawa? Ko daga amminsa Hamza da Jaafar shuwagabannin shahidai, ko a yakokin sa da suka gabata? Babu ko guda daga cikinsu.

Yana tare da mahaifinsa a Basra da Siffin an ga abinda yayi da munafukai. Akwai wani lokaci da ya shiga yaki a siffin sai da babbansa Imam Ali (a) yace, a kamo masa Al-Hassan (a) a dawo da shi, don su ajiyar manzon Allah(s) a wajensa. Ko kamar yadda ya fada.

Sai kuma Abu Sa’id wanda yazo yana aibata Imam Al-Hassan (a), yana cewa: Ya dan manzon All..(s) me yasa ka yi sulhu da Mu’awiya alhali kaine da gaskiya,? Kuma Mu’awiya batacce ne azzalumi?.

Sai Imam (a) ya bashi amsa yana cewa: Ya Aba Sa’id! Shin ni ba hujjan All..ne kan halittunsa ba bayan mahaifi na ?,

Sai ya ce: eee:

Sai yace : Ya Aba Sa’id ! dalilin sulhu na da mu’awiya, shi ne dalilin da ya sa manzon All..(s) ya yi sulhu da, Bani Dhamrah da kuma Bani Ashjaa da mutanen Makka, a lokacinda ya dawo daga Hudebiyya. Wadancan kafirai ne da littafin Allah (a lokacin) amma Mu’awiya da mutanensa kafirai ne da tawilin Alkur’an.

Ya Aba Sa’id ! Idan har ni limami ne wanda All..ta’ala ya nada, bai kamata a wawaita ra’ayi na sulhuntawa ko yaki ba, ko da kuwa mutum bai fahinci hikimar da ke cikin abinda na yi ba.  Shin baka ga cewa, Khidir a lokacinda ya tsaga jirnin ruwa, ya kashe yaro da kuma tsaida bongo, musa ya yi fushi da shi, a lokacinda ya rasa fahintar hikimar da ke cikinsu ba, sai da ya yi basa bayani ya fahinta ba?

Haka nima, kun yi fushi da ni, saboda jahilcinku da hilimar da ke cikinsa. Kuma ba don sulhun da na yi ba, da kuwa babu wani daga cikin shi’armu da zai rayu a bayan kasa sai an kashe shi”.

A nan Imam (a) ya fito fili ya bayyanawa Aba Sa’id kan matsayinsa kamar matsayin manzon All..(s) ba ya aikata kome, sai idan akwai maslaha, amma a wasu lokutan ba kowa ne yake fahintar maslahar ba, sai bayan wani lokaci ko kuma ba zai iya fahinta bag aba daya.

Kuma matsayinda kamar matsayin Halluru (a) da annabi Musa (a) wanda ya rikice, a lokacinda yaga ya bata jirgi, ya kashe yaro ya kuma tsaida Katanga. Amma bayan ya bayyana masa sai ya gamsu ya kuma yi masa biyayya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted