202-Assalamu alaikummasu sauraro barkammu a warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’asni mai girma, ko kumacikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha muttahari ko kuma cikin littafinMathnawi na mailana Jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///.. Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar ImamAl-Hassan Al-mujtaba(a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, mun tsaya a inda muka bayyana yadda wasu daga cikin mabiya Imam Al-Hassan (a) suka kadu suka kuma rikice bayan da labara ya zo masu kan cewa ya sulhunta da Mu’awiya dan Abu sufyan, ya kuma mika masa shugabancin Al-ummar Musulmi.
Mun ambaci Kais dan Sa’ad dan Ubada, daya daga cikin manya manyan kwamandojin sojojinsa. Wanda yake Maskan a cikin kasar Iraki a lokacinda labara ya zo masa kan cewa Imam (a) ya sulhunta da Mu’awiya ya kuma mika masa shugabancin al-ummar Musulmi.
Kais ya rikice ya rasa abinda zai yi, sai ya fadawa sojojinsa, da su zabi guda, ko yaki ba tare da limami ba, ko kuma bai’a ga Dagutu. Sai suka zabi yaki ba tare da Liamami ba. A nan sai Kais ya jasu cikin yaki da sojojin Mu’awiya na wani lokaci sannan, bayan sun yi musayar wasiku da Mu’awiya sai ya dawo cikin hayyacinsa, ya gano cewa ba zai iya samun nasara a kan sojojin Mu’awiya gaba da yaba. Sai ya mika wuya ya je yayi bai’a wa Mu’awiya bayan yasami izinin Imam Al-Hassan (a).
Sai kuma Adiyya dan Hatam atta’ii, wanda shima ya rikice ya je wajen Imam (a) a gidansa a Kufa yana ce masu, bai fahinci abinda yake faruwa ba, ba ta yaya zai fitar da su daga shugabanci na adalci ya mikasu ga shugabanci na zalunci, da sauransu.
Inda Imam(a) ya bayyana masa dalilanda dasuka sa ya dauki shawarar sulhuntawa da Mu’awiya, daga ciki ya fada masa cewa, yana son hana a zubar da jinin mabiyansa na gaskiya ne. sannan munji yadda Addi bai gamsu da abinda Imam Al-Hassan (a) ya fada masaba, ya je wajen Imam Hussain (a) kaninsa, ya bukace shi, ya kawo karshen sulhu da mu’awiya ya nada shi a matsayin kwamandan sojojinu don yakar Mu’awiya. Amma Imam Alhussain (a) ya ki amincewa .
Hakama, Hijru dan Adi al-kindi, mutumin kufa, wanda ya shahara da biyayya ga iyalan gidan manzon Allah (s) amma ya rikice da jin wannan labarin ya zo wajen Imam yana ce masa, ? Shi ma Imam yayi masa bayani don kwantar da hankalinsa. Ya kuma fada masa dalilan da suka sa ya sulhunta da Mu’awiya dan Abusufyan.
Daga bayan mun bayyana cewa Mu’awiya dan Abusufyan ne ya kashe Hijru dan Adiy a lokacinda yaki amincewa ya zagi Imam Amirul muminina Aliyu dan Abutalib (a) daga baya.
Daga karshe mun yi maganar Musayib dan Najba wanda yake cikin sahun farko na mabiya ko masoyan iyalan gidan manzon Allah, wanda shima ya zo a fusace, yana cewa mamakina ba zai kare da kaiba, ta yaya zaka yi ba’a ga mu’awiya kana da mayaka 40,000 da sauransu. Shi ma Imam (a) ya bashi amsa, don kwantar da hankalinsa.
Sai Malik dan Dhamra wanda ya shiga wajen Imam(a) yayi masa magana wacce babu girmamawa a cikinta, kuma mai zafi, amma sai Imam(s) ya amsa masa da cewa ‘Lalle ni na ji tsoron kada a shafe ailummar musulmi daga doron kasa, ina son addini ya kasance yana da mai juyayi don shi.”
Wannan maganar tana da muhimmanci saboda Imam (a) a matsayinsa na mai kare wannan addinin, wanda kuma All..ya azawa nauyin kare shi daga lalacewa, yace yana jin tsoron kada a shafe musulmi daga doron kasa, wannan yana da muhimmanci.
Kafin mu je gaba yakamata wadanda basu san matsayin iyalan gidan manzon All..(s) ba, su sani, kan cewa All..ya zabesu ne don su kare addinin musulunci daga lalacewa, tunda manzon All..(s) shi ne cikamakin annabawa, to kuwa babu wani annabi ko manzo da zai sake zuwa da sakon Alla. Ga mutane.
Imam Al-Hassan (a) yana daga cikin wasiyyan manzon All..(s) don haka All..ya sanarda shi, ko kuma ya sani daga Iyayensa da kuma kakansa manzon All..(s) kan cewa kare wannan addinin daga lalacewa shi ne aikin wasiyyansa.
Don haka muna iya cewa idan ba sulhin Imam Hassan (a) da babu wani musulmi da zai rage a bayan kasa. Kuma da an shafe addinin Muslunci daga doron kasa.
Hatta musulmi wadanda basa bin mazhabar iyalan gidan manzon All..(s), yakamata su sani ba don limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) da hatta addinin da suke yi a yanzu ba zai wanzu ba, ba zai tsira ba.
A wani bangare muna iya cewa, mazhabar iyalan gidan manzon Alla..(s) ita ce addinin musulunci wanda All..ya saukarwa manzon All..(s). amma idan ka dubi bambancinta da sauran mazhabobin musulmi zaka ga cewa bai fi kashe 15-20 cikin % ne kawai.
Wannan saboda kokarinda limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon Alla..(s) suka yi ne.
Daga cikin wadanda suka zo wajen Imam Al-Hassan (a) suka kuma bayyana rashin amincewarsu da sulhun da yayi da Mu’awiya dan Abu sufyan har da wani Bakharije wanda ake kira Sufyan dan Abulaila. Wanda ya shigi wajen Imam (a) a gidansa a Kufa yana magana wacce ta bayyana jahilcinsa da matsayin Imam (a).
Ya shigo yana cewa: Sallama a gareka Ya mai kaskanta Muminai! Imam (a) bai ji dadin abinda ya fad aba sai yace masa.
{Kaitonka Ya Kai Bakharije! Kada ka takura masi, kuma ka san cewa abinda ya san a aikata abinda na aikata shi ne kashe mahaifina da kuka yi. Da kuma dama mani wuka da kuka yi a (madain), da kuma wawason kayakina da kuka yi, Kuma lallei ne, ku a lokacinda kuka je yakin Siffin, addininku yana gaba ga duniyarku, amma a yau kun kasance duniyarku tana gaba ga da addininku. Kaitonka ya kai bakharije, Lalle ni nag a mutanen kufa, mutane ne wadanda baza’a taba dogaro da su ba, ba wanda zai nemi daukaka da su sai wanda ya kaskanta, babu daya daga cikinsu da yake da fahinta guda da wani, hakika mahaifina (a) ya sha wahala a hannunsu, tsanance –tsanance masu daci….. mutanesa sune wadanda suka rarraba addininsu suka zama kungiya kungiya}.
Wannan shi ne siffar mutanen kufa a lokacin ga wanda duk ya karanta tarihi mutanen zai fahinci haka suke. Imam Ali (a) ya dauki lokaci mai yawa yana kiransu zuwa yakar Mu’awiya dan Abusufyan tun kafin lokaci ya kure masu, amma suka ki, har sai da khawarijawa suka kashe shi, suka ci gaba da nuna wadan nan halayensu a lokacinda Imam Al-Hassan (a) ya karbi Jagorancin Al-ummar kakansa, a lokacinda ya fahinci cewa ba zasu sauya ba, sai yazabi sulhu da Mu’awiya don ya kubutar da rayukan sauran muminai da suka rage cikin al-ummar kakansa manzon All..(s).
Sai kuma Bashirul Hamdabi: wanda ya shiga wajen Imam (a) a lokacin ya koma madina daga Kufa, shi ma ya fadi mummunan kalma ga Imam (a). inda yake cewa : Sallama a gareka ya kai mai kaskantar da muminai!.
Sai Imam (a) ya amsa mada da cewa, {wa alaikus salam ka zauan}, sai yace masa {Ni ba mai kaskantamuminai ne ba, sai dai mai daukakasu ne, kuma bai nufi wani abu da sulhun da na yi ba sai don kareku daga kisa, a lokacinda na ga mayakana basa son yaki suna jada baya}.
Sai kuma Sulaiman dan Sard, wanda baya mada’in a lokacinda aka yi sulhun. Yana daga cikin zababbun mabiya iyalan gidan manzon All..(s), a lokacinda ya sami labara sai ya je madina inda ya shiga wajen Imam (a) yana cewa: Amince ya tabbata a gareka ya mai kaskantar da muminai!. Sai Imam (a) ya amsa masa da cewa, {wa alaikumusalam zauna}. Sai Sulaiman ya ce: Mamaki ne da kai baya karewa, ta yaya zaka yi sulhu da Mu’awiya kana da mayaka dubu 100? Daga cikin mutanen kasar Iraki, dukkaninsu suna karban albashi tare da su har da wasu kama da su, na daga yayansu da bayinsu? Wannan banda shi’ar da suke Basra, da mutanen Hijas, … ….
A lokacinda ya kammala maganarsa, sai wasu daga cikin shi’ars Imam (a) wadanda suke wurin suka goyi bayan Sulaiman dan Sard, suna wasu maganganu irin tasa.
Imam (a) ya basu amsa da cewa: {Bayan haka, ku mabiyammu ne, masoyammu ne, wadanda muka sansu da yi mana nasiha, suka luzumtarmu, suke kuma tsayawa don mu kuma na fahinci abinda kuka fada. Sai dai da na kasance na yi abinda nayi din na duniya, to ku sani da Mu’awiya ba zai rinjayeni ba, saboda bai fi ni hakuri a fagen fam aba, ko ya fine jarunta ba, sai dai ra’yi na ba irin taku ba, sannan ina shaida maku kan cewa ba abinda nake nufi da abinda na yi face hana zubar da jinanenku, da kyautata tsakaninku, ku ji tsoron All..ku yarda da kaddaran All.., ku mika al-amari ga All..ku luzumci gidajenku, ku kama hannayenku, don mutanen kirki su huta, ya huta daga fajiri, wannan tare da cewa, mahaifi na ya sha fada mani kan cewa, Mu’awiya zai karbi shugabancin wannan al-ummar, ina rantse maku da All.. da mun tafi da duwatsu don yakarsa, mun tafi da dukkan itatuwa don yakarsa, bana shakka sai ya sami nasara a kammu, shi All..ba wanda yake kwance hukuncinsa, ba wanda zai maida abinda ya hukunta.
Amma zancenka ya mai kaskanta muminai, na rantse da All..da ku kaskanta ku sami lafiya ya fiye mani da izza wacce daga karshe za’a kashe ku, idan All..ya mayar mana da hakkimmu a cikin ruwan sanyi zamu karbeshi, …. }.
Masu sauraro anan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan Allah ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.