201- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na AYa. Shahid Murtadha Muttahari ko kuma littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddin Rumi ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.
////..Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikinshrimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Al-Hassan Aljtaba (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s), inda kawo maku yanda sulhunsa da Mu’awiya dan Abusufyan ya yi nauyi wa masu ikhalasi daga cikin shiarsa ko mabiyansa, wadanda suke fatan karawa da sojojin mu’awiya ko nasara ko shahada. Amma a lokacinda suka ji cewa Imam Al-Hassan ya sulhunta na Mu’awiya kuma zai mika masa ragamar shugabancin Al-Ummar musulmin sai sun kasa fahintar abinda yake faruwa.
Wasu daga cikinsu, kamar Kais dan Sa’ad dan Abuda. Ya cewa sojojin da suke tare da shi su zabi guda ko biyayya ga Tagutu Mu’awiya dan Abusufyan ko kuma su yi yaki ba tare da Limami ba.
Mun bayyana cewa sun zabi yaki ba tare da Limami na da farko, amma bayan wani lokaci, bayan musayar wasiku da mu’awiya ya amince ya shiga cikin abinda limaminsa ya shiga. Sai dai ya nemi afwa wa kansa da mayakansa daga Mu’awiya wanda kuma ya amince ba tare da jinkiri ba.
Sannanbayan shigowarsa wajen Mu’awiya dan Abusufyan ya nemi izinin Imam Al-Hassan (a) kafin yayi masa bai’a.
Har’ila yau mun yi maganar sauran fitattun yan shia mabiya iyalan gidan manzon All..(s) wadanda suka hada da Hijru dan adiya, da Al-musayyib Dan Najba, duk sun je wajen Imam Al-Hassan (a) a Kufa kafin ya kama hanyarsa zuwa Madina sun yi masa kukan kan yadda suka takuru da sulhun da yayi da Mu’awiya dan Abu sufyan.
Imam ya bayyana masu cewa ya yi sulhu da Mu’awiya ne don karesu daga a zubar da jininsu, ko a cutar da su. Kuma ya dauki matakan sulhuntawa da Mu’awiya ne ba da zabin kansa ba, sai dai al-amura ne suka hukunta ya yi hakan. Banda haka ya fada masu cewa baya al-amura bisa son zuciyarsa ko ransa saboda shi ma’asumi ne, baya kuskura.
Jarrabawan da Imam Al-Hassan (a) ya fuskanta bai takaita ga sulhu da Mu’awiya dan Abusufyan kadaiba, said ai jarrabawa mafi muni da ya fuskanta dangane da wannan sulhun shi ne suka daga manya manyan masoyansa shiar Ahlul bait (a) wadanda a rikice suka gasa masa maganganu masu daci kan yadda ya amince da sulhuntawa da Mu’awiya. Banda haka Hattawa wadanda dama suna adawa da shi kamar Khawarijawa sun yi amfani da wannan damar don sukarsa. Wani lokacin har tare da kaskantashi da kuma wawantar shi (a). Wannan jarrabawar ta yiwa Imam Nauyi sosai fiye da sulhun kansa.
A matsayin Misali.
01-Hijru dan Adiy Alkindi daya daga cikin fitattun mutanen Kufa kuma wanda ya shahara da son iyalan gidan manzon Allah (s) ya kadu da jin labarin sulhuntawar Imam Alhassan (a) da Mu’awiya da kuma mika masu shugabancin al-ummar musulmi, ya shiga wajen a birnin Kufa kafin ya koma madina yana cewa:
Amma wallahi da naso ace ka mutu, mu ma mutu tare da kai kafin ranar sulhu bamu ga wannan ranar ba. Amma sai gashi mu mun koma da abinda bama so, su kuma son koma da abinda suke so.
Bamu san yadda aka yi Hijru dan Adiy, duk tare da sanin matsayin iyalan gidan manzon Allah (s) ya iya furta wannan maganar daga bakinsa a gaban limami mai tsarki ba?. Amma ganin yadda al-amarin ya kidime mutanen da dama, muna iya cewa ya fita daga hayyacinsa ne, kafin ya fadi wadan nan munanan magan gani, har yake fatan mutuwar Imam (a) kafin tabbatar sulhu.
Amma Imam Alhassan (a) ya hadiye fushinsa, yak ama hannun Hijir dan Adiy zuwa wata zawiya a cikin gidansa sannan ya kara yi masa bayanin dalilan da suka sa yayi sulhu da Mu’awiya dan Abusufyan.
Yana cewa:
{Ya Hijir ! na ji maganarka a gaban Mu’awiya, kuma ba ko wani mutum ne yake son abinda kake so ba, ko ra’ayinsa kamar ra’ayinka ba. Lalle ni ban amince da Sulhu bas ai don kare jininku daga zubarwa, Allah mai girma da daukaka yana cikin sha’aninsa a ko wace rana}.
Imam (a) ya bayyana cewa ya sulhunta da Mu’awiya ne don hana zunar da jinin muminai, kamar Hijar da masu kama da shi a cikin shi’arsu, masu Imani da ikhlasi da kuma sanin matsayinsu. Ya bayyana cewa baida mataimaka a cikin mutanen Kufa isassu kamar Hijir dan Adiy da makamantansa a cikin masu reya goyon bayansa.
Kamar yadda zamu gani nan gaba, daga karshe Hijir dan Adiy ya yi shahada a hannun Mu’awiya dan Abu sufyan, don yaki ya zagi Imam Amirul mumina (a) da bakinsa. Wanda yake bayyana irin Imani da Ikhlasinsa da biyayya ga Iyalan gidan manzon Allah (s).
02-Adiy dan Khatam Atta’ii. Wanda ya kasance daga cikin fitattun sahabban manzon Allah(s) . Shine shugaban Kabilarsa ‘Attai’, ya bayyana Akhasinsa ga ayalan gidan manzon Allah (a) a wurare da dama. Daga cikin yayansa kuda uku ya rasa a tsakanin yakin Jamal da Siffin a yakar makiyan iyalan gidan manzon Allah (s).
A lokacinda Adiy dan Hatam Atta’ii ya shiga wajen Imam Al-Hassan (a) ya yi ladabi a maganar da shi. Inda yake cewa:
Ya dan manzon Allah (a)! Na so ace na mutu kafin abinda na gani, ka fitar da mu karkashin adalci ka mika mu zuwa zalunci, mun bar gaskiyanda muka kasance a kanta, mun shiga karkashin zaluncin da muke gudu daga gare shi, mun kaskantar da kammu, mun amince da kaskancin da bai dace da mu ba. Wannan maganar ta sosa zuciyar Imam (a) ta sa shi bakin ciki, sai ya tashi ya fara bayyanawa Adiy dan Hatam abinda ya say a sulhunta da Mu’awiya dan Abusufyan yana cewa:
{Ya Adiy ! Lallai ne naga mafi yawan mutanen suna sun sulhu, basa son yaki, ni kuma bana son tilasta masu abinda basa so, don haka sai na sulhunta don hana kisa da zubar da jinin masoyammu. Da haka kuma na ga yakamata in dage wannan yakin zuwa wani lokaci, kuma Lalle Allah yana cikin sha’aninsa a ko wace rana}.
Imam (a) ya bayyana masa yadda sojojinsa suka kosa da yaki, da kuma son zaman lafiya, da zaben sulhu maimakon yaki. Ya fada masa cewa, yana kan bakarsa ta yakar Mu’awiya amma a wani lokaci nan gaba, a sanda yake fatan samun nasara a kansa.
A lokacinda Adiy y agama sauraron Imam Al-Hassan (a) bai gamsu da maganarsa ba, sai ya tashi ya je wajen kaninsa Imam Al-Hussain (a) , ya sameshi tare da Ubaidatu dan Umar, sai ya jira shi, a lokacinda ya karasa zuwa wajensa sai yace (Ya baban Abdullahi ! Kun sayi kaskanci da daukaka, kun karbi kadan kun bai mai yawa, mun yi biyayya a yau, amma mun saba na zamani mai tsawo, ka bar Imam Alhassan(a) da ra’ayinsa na sulhu, ka tare masoyanku a Kufa da wasu wurare, ka sanyani da wannan abokina shugabancin sojojinka, dan Hindu ba zai fark aba sai ya ga muna yakarsa da takubbammu). Sai Imam Al-Hussain (a) ya bashi amsa da cewa:
{Lalle mun rika mun yi bai’a, kuma mun dauki alkawali, babu wata hanya ta kwance bai’armu}.
03-Sai kuma Musayyib Dan Najba, wanda ya kasance cikin sahu na farko a cikin masoya iyalan gidan manzon Allah (s) a Kufa, ya je yakin Qadisayya, ya kuma je yaki tare da Aliyu dan Abitalib (a) gaba daya a lokacinda khalifancinsa. Sannan daga karshe yayi shahada a yakin ‘Ainul-Warda tare da Sulaiman dan Sard don neman fansar jinin Imam Al-Hussain (a).
Musayyib dan Najba ya tasirantu da Sulhun Imam Al-Hassan (a) da Mu’awiya, jikinsa ya muta, ya kuma karya sosai da shi. Ya shiga wajen Imam (a) yana cewa (Mamakin aba zai kare da kai ba! Ta yaya zaka yi bai’a ga Mu’awiya kana da mayaka 40,000?. A abinda naji, bai yi haka bas ai don kai ne. ) sai Imam yace masa: {Me kake gani?} Sai yace: (Ina ganin ka koma inda kake a da, ga shi ya rika ya sabawa abinda kuka cimma tsakaninka da shi).
Sai Imam (a) ya tashi ya zauna don yi basa Karin bayani. Yana cewa {Ya kai Musayyid! Lalle da ina nufin nemen duniya -da abinda na aikata- da kuwa Mu’awiya ba zai fi ni hakuri a yaki ba, ko kuma mafi tabbata a fagen fama ba, sai dai ni ina bukatar kyautata al-amarinku, da hana kashe-kashe a tsakaninku}.
A nan Imam (a) ya bayyanawa Musayyib kan cewa da duniya yake nema da kuwa Ma’awiya zai sami nasar a kan Mu’awiya, saboda bai fi shi hakuri a yaki ba, bai fishi tabbata a fagen fama ba, amma kamar yadda kowa ya sani Mu’awiya na yaudara da karya da kha’inci, wanda bai dace ga limami yayi haka ba. Don haka yana kan tafarkin mahaifinsa Amirul mumina (a) na neman adalci da gaskiya da kuma yardarm Allah a dukkan abinda zai aikata.
Masu sauraro a nan zamu dakata a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan Allah ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.