207-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin Al-Qur’ani mai girma ko cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.
///…Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Almujtaba(a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi maganar, rashin amincewar surukantaka da banu uammaya wanda Imam Al-Hassan (a) yayi.
Inda da farko Mu’awiya dan Abusufyan ya aikawa walinsa da ke Madina a lokacin, wato Marwan dan Hakam, zuwa wajen Abdullahi dan Jaafar dan ammin Imam Al-Hassan (a) ya nemawwa dansa Yazid auren diyarsa masi suna Zainab.
Mun bayyana cewa a lokacinda sakon Mu’awiya ya isa wajen Marwan ya aikawa Abdullahi dan Jaafaru ya zo fadarsa a Madina, a lokacinda ya karaso, sai Marwan ya fada masa sakon Mu’awiya dan Abusufyan gareshi na bukatar ya aurawa dansa Yazid diyarsa wacce ake kira Zainab.
Tare da cewa zai biya sadakinta bida duk abinda shi amdullahi dan Jaafaru ya ambata, tare da kuma biyan dukkan basussukan da ke kansa, ko menene yawansu.
A lokacinda Abdullahi dan Jaafaru ya ji hakan, sai ya fadawa Marwan cewa, auren yayansu mata yana hannun Imam Al-hassan (A) ne, ya nemi auren daga wajensa.
Kuma munji yada Marwan ya je wajensa ya fada masa sakon mu’awiya ga Abdullahi ga kuma abinda Abdullahi ya fada masa, sai Imam Al-Hassan (a) ya ce masa ya je ya kira duk wanda zai kira don su saurari amsar da zai bashi. Sai Marwan ya sa aka kira masa wasu daga cikin dangin Banu Umayya da kuma wasu daga cikin dangin Banu Hashin, ya tara su a gaban Imam Al-Hassan (A) ya kuma tashi yayi masu khuduba, a cikin khudubarsa, yayi maganar sakon Mu’awiya ga Abdullahi dan Jaafar sannan ya bayyana manufar auren da cewa, don kyautata tsakanin dangin banu Umayya da banu Hashim ne … kuma yazid yana shayarda mutanen ruwa da darajarsa a wajen All..).
Sannan munji amsar Imam (A) gare na kan karyayyakin da yayi kan Matsayin Yazid, daga karshe ya fada masa cewa, ya rika ya aurad da Zainag gad an amminta Qasim dan Mohammad dan Jaafaru.
Daga nan Marwan ya kidime yana da cewa, banu hashin sun yaudareshi, amma yayi zai yi? A dole ya aikawa Mu’awi ya fada masa abinda ya faru. Suka kuma hakura.
A cikin wani tarihi ance Mu’awiya ya aiki wani ya nema masa auren kanuwar Imam Al-Hassan (a) ko kuma diaysa, a lokacinda mai sakon yazo, sai ya fada masa cewa, su basa aurad da matansu sai tare da amincewarsu, don haka ya je wajenta. Alokacinda dan sokon ya hadu da ita ya fada mata bukatarsa, sai tace masa hakan ba zai taba faruwa ba, har zuwa lokacinda mu’awiya ya zama fir’aurna ya kuma kashe yayansu maza ya kuma raya yayansu mata. Sai ya dawo yana fadawa Imam Al-Hassan (a) kan cewa, ka aikani zuwa wacce take kiran (amirulmuminina) Far’auna? Daga karshe Imam Al-Hassan (a) ya fada masa wani hadisi daga manzon All..(s) yana cewa makiyansu wadanda suke fusatar da su zasu zo ranar kiyama a tabkin al-kauthara sai a koresu da bulala daga daga wuta.
Dangane da wannan, Mu’awiya dan Abu Sufyan yayi wani kokari na aure daga dangin Banu Hashim amma Amirulmuminina (a) ya hana shi. Yadda labarin yake shi, kafin wafatin Fatimah (s) diyar manzon All..(s) ta fada masa cewa idan ta rasu, ya auri Umamah diyar yayarta Zainab diyar manzon All..(s), daga mijinta Abulass. Don zata kula da yayanta Al-hassan da Al-Hussain (a) da sauransu kamar yadda zata kula da su.
Don haka bayan wafatintsa, ko shahadarta(s), Imam Ali (a) ya auri Umama, wasu sunce ta haifar masa da wanda ake kira muhammada, sannan a lokacinda Abdurraman dan Muljam Almuradi La’anenne, ya sari shi(a) da takobinsa a cikin watan Ramadan shekara ta 40 bayan hijira a Kufa. Imam Ali (a) ya ya ga cewa ba zai rayu ba sai ya kira Umamah, ya ce mata, idan zaki yi aure a bayana ki uari Mugira dan Naufal dan Ubaidullahi dan Haritha dan Abdulmuttalib.
Kakan mugira wato Ubaidullah dan Hariritha shi ne shahidi na farko a yaki a Badar, sannan jikansa Mugira wanda Amirulmuminina aliyu dan Abitalib (a) yacewa matarsa Umama ta aureshi, malami ne masanin addini, ya kuma taba bashi aikin alkalanci a lokacin da ya rike khalifanci. Kuma abinda yasa ya fata mata hakan shi ne, baya son mu’awiya ya aureta a bayansa. Sai yayi alfakhari ya auri jikan manzon All..(s).
Abinda kuma ya faru Kenan bayan shadar Imam Ali (a) da kuma sulhun Imam Al-Hassan da Mu’awiya bayan watanni 6, sai mu’awiya ya aikwa Umama yana son aurenta sai taki, sannan ta je ta fadawa mugira ga wasiyanta da Imam Ali (a) ya fada mata kafin shahadars, sai mugira ya aureta.
Don haka banu umayya sun yi kokari su auri danganen manzon All…(s) don su ci duniyarsu da hakan, amma limai daga cikin iyalan gidan manzon All..(s) sun hana hakan faruwa. Sanna a lokacin sarakunan Abbasiyawa ma, sarki Ma’amun dan Sarki Harunar Rasheed sarki na 7 daga cikinsu, ya aurarwa Imam Mohammadul Jawad liamai na 9 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) diyarsa wacce take Ummul Fadle. Wacce yana son ta zama mahaifiyar limami na 10, daga cikin iyalan gidan manzon All..(s), amma All..T bai su haka ba don bata haifu ba, sannan mahaifiyar Imam Aliyul Hadi wanda shi ne limami na 10 ta zama wata kuyanga mai suna Samana (Susan), wacce ta fito daga kasashen larabawa arewacin Afirka, ko susan Al-magribiyya. Don haka ummul fadle ta ci gaba da kasancewa, mai bada rahoton abinda yake faruwa a gidan Imam Alyul Hadi (a) ga sarakunan Abbasiyawa.
Sai kuma ziyara ta farko wacce Mu’awiya dan Abusufyan ya kai Madina bayan sulhi da Imam Al-hassan (a), inda ya shiga garin ya ga kuma yanda mutane suke girmama Imam(a) hakan ya mata basa rai. Sai ya kira Abu’aswad addu’ali da kuma Dhahhak dan Kais Al-Fakhari don shawartansu kan yanda zai yi da Imam Al-Hassan (a) don kaskantashi a cikin mutanen Madina.
A lokacin da ya kammala sai Abuaswad Addu’ali ya ce masa: (Ra’ayin amirulmuminina ya fi, amma duk da haka ina ganin, kada kayi wani abu na kaskanta shi, don duk abinda za ka fada dangane da shi masu sauraro zasu dauke shi a matsayin hasada ce gareshi, kuma zasu kara daukakashi saboda haka. Kuma Imama Al-Hassan matashine, ina jin tsoron zai mayar maka da martani, wand aba zai maka dadi ba, …ya kuma bayyana wasu laifuffuka. … sai dai idan ka san ya aikata wani aibi, Don haka maganarka dangane da shi tana iya zama falala gareshi, … zuwa inda yake cewa, kada ka takaleshi ya amirulmuminina.)
Wannan maganar Abu Aswad Addu’ali Kenan, wanda yayi masa nasiha, ya kuma bayyana masa hatsarin duk wata magana da zai yi dangane da Imam Al-Hassan (a) tana iya kunyata shi a cikin al-umma.
Dhahhak dan Kai alfikhri ya goyi bayansa, ya yi magana ya kuma kaskanta Imam Al-Hassan (a).
Amma mu’awiya ya karbi nasihar Kai dan Dhahha, saboda a lokacinda Jumma’a ta same shi a madina, ya hau kan mimbari yana khuduba, ya yabi All..(s) yayi salati ga manzon All..(s) sai ya ambaci Amirulmuminina Aliyu dan Abutalib(a), sai ya aibata shi a cikinta, sannan yace..
Ya ku mutane, lalle wasu yara daga kuraishawa, wawaye da … rayuwa ta yi masu tsanani, kaddarorin All..a kansu sun wahalar da su, sai shaitan ya riki kawukansu wararen zama, sannan harsunansu suka zama asalinsa, yayi kayau ya kuma kenkeshe yaya a cikin zukatansu, ya daukaka a cikin zukantansu, sai ya kaisu ga kura kurai, ya kawata masu laifuffuka, ya kuma kakantar da su daga ganin hanyoyi, ya nuna masu hanyar tsokana da zalunci, da karya da buhtani, su masu tarayya ne da shi, kuma ya zama majibincin al-amarinsu {Kuma wanda shaitan ya zama abokinsa, aboki ya munana}, aya zama mai horar da su, All..ne madogara.
Sai Imam Al-Hassan (a) ya yunkura ya tashi, yana masa raddi. Yana cewa. {Ya ku mutane! Wanda ya sanni ya sanni wanda bai sanni ba, nine Al-Hassan dan aliyu dan Abitalib(a), ni dan annabin All.. ne, kuma ni dan wanda aka sanya msa kasa wurin sujada da kuma tsarki, kuma nina dan fitila mai haskakawa, ni dan mai bushara mai kuma gargadi, kuma ni dan cikamakin annabawa ne, kuma shugaban manzanni, kuma shugaban masu tsoron All.., kuma ma’aikin Ubangijin talikai, kuma ni dan wanda aka aiko ga aljanni da mutane, ni dan wanda aka aiko mai jinkai da talikai ne}
Wadan nan kalaman sun yi tsanani ga mu’awiya dan Abusufyan sai ya yanke maganarsa, Yace (Ya Hassan na horeka da siffar dabino mai laushi)!.