206-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo mako kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan, wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu, a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Almujtaba (a) dan Fatima(s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, mun tsaya a inda muka bayyana yanda Imam Al-Hassan (a) ya aikawa Ziyar dan Sumayya wasika yana neman ya baci ceton Sa’id dan Sarh, mutumin Kufa wanda ya zo Madina yana kuma neman ceton Imam Al-Hassan daga sharrin Ziyad wanda yake son kashe shi. Sannan mun ji cewa bayan da wasikar Imam (a) ya isa wajen Ziyar yana umurtan Ziyad ya bashi ceton Sa;id dan Sarh, da kumaumurnin ya sake matansa da yayansa da ya kama ya kuma sake gina masa gidansa da ya rusa ya kuma mayar masa da dukiyoyinsa da ya kwace, sai Ziyad yayi fushi saboda bai kirashi da dan Abusufyan ba.
Daga nan sai ya mayar masa da wata wasika mai zafi wacce ya aibata Imam Al-Hassan (a) a cikinta da bashi umrni al-hali shi sarki ne, ya kuma gabatar da sunansa a kan sunan sa. Har’ila yau Ziyar- don kiyayya ga Imam Ali (s) ya kira Imam Al-Hassan ya danganta shi da mahaifiyarsa Fatimah (s).
A lokacinda wasikar Ziyad ta isa wajen Imam (a) a Madina ya karantata ya fahinci abinda Ziyada yake nufi, wato yana son ya kirashi da Ziyad dan Abusufyan, sai ya rubuta wasika ga Mu’awiya ya fada masa abinda ya faru, sannan ya sanya wasikar Ziyar da ya mayar masa yana aibata shi.
A lokacinda Mu’awiya ya karanta wasikar Imam Al-Hassan (a) ya kuma karanta wacce Ziyad ya aikawa Imam(s) yana aibata shi, sai ya dauki Alkalami, ya rubutawa Ziyad Wasika, inda a ciki yake bayyana masa mamakinsa da yadda yake magana da Imam kamar yanda yayi.
Sann ya bashi umrni ya aiwatar da dukkan umurnin Imam a gareshi. Ya kuma bayyana masa kurakuran da yayi a wasikar da ya rubutawa Imam, inda yake fada masa, cewa, shin bai san cewa kiran Imam Al-Hassan dan Fatima (s) ya fi ye masa da dangantashi da babansa ba. Ko bai san cewa fatimah diyar manzon All…(s) bace? Da sauransu.
A yau zamu tashi daga inda Imam (a) ya hadu da Habab dan Muslimu Alfehri daya daga cikin jiga jigan Qurasihawa, kuma ma’aikacin Mu’awiya dan Abusufyan. Wanda kuma yake matukar kiyayya ga iyalan gidan manzon All..(s).
Imam Alhasan (a) ya hadu da shi a dawafin dakin Kaaba, sai yace masa {Ya Habibu sau da dama kana tafiya ba a biyayya ga All..ba}.
Da farko shi Habibu yana daga cikin mutane mafi kusa da Mu’awiya dan Abusufyan, baya rabuwa da shi, yana tare da shi a yakin Siffin da kuma sauran wurare, An fi saninsa da Habiburrumi, saboda yawan shigarsa ruma. Sannan Mu’awiya ya bashi walin Armenia, ya ci gaba da kasancewa a can har ya mutu a shekara ta 42 bayan hijiya.
Don haka sai Habibu ya amsawa Imam Al-Hassan (a) da ce wa ‘Amma banda yanda nayi da babanka, shi kam ba haka ba ne’ wato shi kam biyayya ga All..ne. Sai Imam (a) ya masa da cewa {Ai har da shi, na rantse da All.., sai dai ka yi biyayya ga Mu’awiya a kan duniya yar kadan kuma mai gushewa, idan ya baka duniya, amma ya hanaka lahiranka, da ace idan ka aikata kana fadin alkhairi da ya fi maka, kuma da al-amarinka zai kasance kamar inda All..Ta yake cewa {Da kuma wasu wadanda suka yi ikrari da zunubansu, sun garwaye ayyuka kyawawan ayyuka, da wasu munana } sai dai baka kasance haka ba, ka kasance kamar yanda All..T yake cewa {A’aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.}} Sai Imam (a) ya tafi ya kyaele shi.
Sai kuma batun neman surukantaka da Banu Hashim, inda Mu’awiya dan Abu sufyan ya aikawa walinsa a Madina, Marwan dan Hakam, ya nema masa auren Zainab diyar Jaafaru dan Abitalib ga dansa Yazid. A lokacinda sakon Mu’awiya ya isa hannun Marwan sai ya aika aka kira masa yayar Zainab, wato Abdullahi dan Jaafaru, a lokacinda ya zo, sai Marwa ya fada masa abinda Mu’awiya yake so a wajensa, na awrawa dansa yaziz Zainab diyarsa. Tare da cewa, shi ne mahaifinta ne, kuma sadakinta duk abinda ya fada, tare da biya masa dukkan basusukan da suke kansa ko mene uawansu, kuma wani mataki ne na sulhuntawa tsakanin kabilun Banu Hashim da Banu Umayya.
A lokacin Abdullahi yaji haka, sai yace masa, Al-amarin matammu yana hannun Imam Al-Hassan (a), ka nema masa ita daga wajensa. Sai Marwan ya je wajen Imam Al-Hassan (a), ya fada masa ga abinda Amirul muminina Mu’awiya yake so, sai Imam (a) yace masa {Ka tara duk wadanda kakeso} , sai marwan ya tashi ya tare dangane Banu Umayya da dama, ya kuma tara wasu daga cikin banu Hashim, yayi masu khuduba yana cewa, ‘Bayan haka, Amirul muminina Mu’awiya ya umurceni in nemawa dansa auren Zainab diyar Abdullahi dan Jaafar, wa dansa Yazidu dan Mu’awiya, bida duk abinda mahaifinsa ya fada na sadaki, da kuma biyan basussukansa ko menene yawansu, saboda kuma sulhu tsakanin kabilun Banu Hashin da Banu umayya, kuma Yazidu dan Mu’awiya Kufu’in wacce baida kufu’i ne,
Na Rantse da All.., wadanda suke maku hasada da surukantaka da Yazid sun fi wadanda sukewa yazid ya aura daga cikinku. Yazidu yana daga cikin wadanda ake shayar da mutane ruwan sama saboda shi’.
A nan shi marwan yana ganin matsayin mutane shi ne girman da matsayin da suke da shi a wannan duniya ne. Bijiro da wannan ya bayyana wawtarsa da jahilcinsa, a gaban Hashimawa da kuma Banu umayya wadanda ya tara. Sai Imam (a) ya mayar masa kan karyayyakin da ya fada. Yana cewa bayan gabatarwa {Amma abinda ka ambata na duk abinda babanta ya fada na sadaki, mu bama sabawa sunnar manzon All..(s) acikin auradda yayansa iyalan gidansa da matansa, amma dangane da biyan basussukan mahaifinta, yaushe ne, matammu suka biya basussukan iyayensu da sadakinsu, amma sulhuntawa tsakanin kabilu biyu, mu mun yi adawa da ku don All..ne ba zamu yi sulhu da ku don duniya ba, Amma zancenka na cewa, Yazid kufuin wacce bata da kufu’i, ai wadanda suke kasance kufu’insa a jiya sune kufu’insa a yau, sarautar da ya samu bai kareshi da kome ba, amma dangane da cewa, masu hasadarmu kan yazidu sun fi yawa a kan wadan suke hasadar ya aura daga cikimmu, idan har khalifanci ne ya gabaci annabci ana mana hasada, idan kuma annabci ne ya gabaci khalifanci shi ma ana mana hasada. Amma zancenka na cewa ana shayar da mutane ruwa da Yazidu, wannan bai taba kasancewa ba sai ga iyalan gidan manzon All…(s) }
Bayan ya kammala karyata dukkan karyayyakin da Marwan dan Hakam yayi, amaganarsa sai Imam (a) ya bayyana hukunci na karshe inda yake cewa,
{Mun ga cewa zamu aurad da Zainab ga dan amminta Qasim dan Muhammad dan Jaafaru, hakaki mun rika mun awaradda ita gareshi, kuma na sanya sadakinta fili na a madina, Mu’awiya ya bani dinari 10,000 a kansa amma na ki}.
A lokacinda Marwan ya ji haka, sai ba tare da sonsa ba ya tashi yana kuwa, yana cewa: shin yaudarce ya ku Banu Hashim,?
Amma Marwan ne yafi cancanta da Yaudara, Imam (a) yayi abinda ya dace, yayi Alkhairi tunda yaki ya aurar wa Yazid Fasiki mashayin giya daga matan banu hashim.
Bayan haka Marwan ya rubutawa Mu’awiya wasika yana fada masa binda ya faru, a lokacinda Mu’awiya ya karanta wasikar sai yayi bakin ciki da hakan. Sai yana cewa:
‘Mun nemi aure daga cikinku, kun hanamu, da kum nemi aure daga cikimmu da bamu hanaku ba.
Hakiki Imam Al-Hassan (a) ya san manufar mu’awiya na daukaka dangin banu umayya, don haka ne ya dauki matakan wargaza aikinsa. Banda haka labari yazo masa kan cewa, mu’awiya na fada
” Bai kamata a sami wani Bahashime wanda ba mai yawan kyauta ba, ko ba umayye wanda ba mai hakuri ba, ko ba Zubaire wanda ba jarumi ba, ko kuma ba-makhzume wanda ba rikitacce ba ‘.
Ya kuma fahinci cewa manufar Mu’awiya itace, wargaza dangin Hashimawa ne, da daukaka sauran kabilun larabawa a kanta.
A wani hadinin wanda Khawarizmi ya kawo a cikin littafin Maktalul Husain (a) yana cewa, ya zo a cikin Majamauz Zawa’id Jz 4 Sh 278 daga Mu’awiya dan Khudaij yana cewa: Mu’awiya dan Abu sufyan ya aike ni zuwa wajen Imam Al-Hassan dan Ali (a) in bukaci ya aurar wa Yazid diyarsa ko yar’uwansa, sai na je masa na kuma ambaci Yaziz, sai yace mani: mu mutane ne wadanda bama auradda matammu sai mun nemi izininsu, sai na je wajenta na ambata mata Yazid, sai tace: Na rantse da All.. hakan ba zai faru ba, sai mutuminka ya zama a cikimmu kamar yanda Fir’unna ya zama a cikin banu Isra’ila, ya yanki mazajemmu ya kuma raya matammu, sai yace na koma wajen Imam Al-Hassan (A) na ce masa,: Ka tura ni zuwa wajen wacce take kiran Amirul muminina Fir’auna? Sai Imam (a) ya ce: Ya kai Mu’awiya ( dan Khudaij) ! ina maka kashedi da ka kiyaye fushimmu, Lalle manzon All..(s) yace, ba wanda zai fusatamu ko yayi hasada damu sai an koreshi daga tabkin alkauthara da bulala na wuta.
Masu sauraro saboda kurewar lokaci a na zamu dasa aya a cikin shirummu na yau sai kuma wata fitowa idan All ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamtullahi wa barakatuhu.