Search
Close this search box.

Kenya: Shugaba Ruto Zai Bude Kofar Tattaunawa Da Matasa Masu Zanga Zanga

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya bayyana anniyarsa ta shiga tattaunawa ta hankali da matasan da suke zanga zanga a makon da ya gabata, saboda

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya bayyana anniyarsa ta shiga tattaunawa ta hankali da matasan da suke zanga zanga a makon da ya gabata, saboda sabbin harajin da ya bullo da su a kasar.

Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya bayyana cewa kungiyoyin matasa masu kare hakkin biladama da dama a birnin Nairobi babban birnin kasar da kumam wasu manya manyan biranen kasar sun fitoi zanga zangar nuna rashin amincewarsu da sabbin harajin.

Labarin ya kara da cewa ya zuwa yanzu dai an ce mutane 2 sun mutu a yayinda wasu kimani 200 sun ji rauni sanadiyyar karawa da jami’an tsaro a ranar 23 ga watan yunin da muke cikin.

Matasan sun bukaci a fito sabuwar zanga zanga a yau Talata 25 ga watab yuni, don takurawa gwamnatin Ruto da janye wadanan sabbin harajin da ya bullo da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments