Kasashen Larabawa Sun Yi Tir Da Matakin Isra’ila Na Hana Shigar Da Kayan Agaji A Gaza

Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna

Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna masu bayyana hakan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas da kuma dokokin kasa da kasa.

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a cikin wata sanarwa ta ce “Masar ta yi Allah-wadai da kuma yin tir da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na dakatar da agajin jin kai ga Gaza, tare da yin amfani da shi a matsayin wani makami na cin zarafi da azabtarwa.”

Masar ta kuma yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da duk wani agajin jin kai a zirin Gaza a matsayin “ketare iyaka” na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.

Ma’aikatar harkokin wajen Masar a cikin wata sanarwa da ta fitar “ta yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na hana agajin jin kai da mashigin da ake amfani da shi wajen kai agaji.”

Ma’aikatar ta ce “wadannan ayyukan sun saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta, dokar jin kai ta kasa da kasa, Yarjejeniyar Geneva ta Hudu, da dukkan ka’idojin addini.”

Yarjejeniyar Geneva ta hudu da aka amince da ita a shekarar 1949 bayan yakin duniya na biyu, ta ta’allaka ne kan ba da kariya ga fararen hula, ciki har da yankunan da aka mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments