Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin alkahira a jiya Lahadi, inda ya sami kyakkyawar tarba daga Abdulfattah al-Sisi.
Ziyarar ta shugaban kasar Faransa a Masar tana a karkashin tattaunawar da aka bude ne a yau Litinin tare da kasar Jordan da kuma ita kanta mai masaukin baki akan halin da Gaza take ciki.
Yin wannan taron dai ya biyo bayan sake dawo da yaki da HKi ta yi ne a Gaza, saboda ta ki amincewa da bude shafi na biyu yarjejeniyar tsagaita wutar yaki.
A yau Litinin shugabannin kasashen na Masar da kuma Faransa sun yi tir da sake dawo da yaki da Isra’ila ta yi a zirin Gaza, haka nan kuma kin amincewa da shigar da kayan agaji a cikin yaki.
Ana sa ran cewa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron zai ziyarci yankin Arisha mai nisan kilo mita 50 daga zirin Gaza saboda ya gana da ma’aikatan agaji a suke da sansani a wurin.
Bayan kammala taron nasu, kasashen uku sun fitar da bayani na yin kira da a tsagaita wutar yakin Gaza da gaggawa, da kuma bude kafar ci gaba da aikewa da kayan agaji zuwa yankin.
Tun da fari, shugabannin kasashen Masar da Faransa sun yi taron manema labaru da su ka nuna kin amincewarsu da duk wata siyasa ta korar Falasdinawa daga kasarsu.