Kwamandan rundunar Kudus dake karkashin IRGC Birgediya janar Isma’ila Ka’a’ni ya bayyana cewa; Iran ta samu nasara, kuma nasara ce wacce za ta dore da yardar Allah.
Birgediya janar Isma’ila Ka’a’ni wanda ya halarci jana’izar shahidan ta’addancin HKI ya bayyana cewa; Daga yanzu zuwa gaba abinda yake gabanmu shi ne ci gaba da samun nasarori.
Haka nan kuma ya ce; Idan har aka samu hadin kai, aka yi aiki tare a tsakanin al’ummar kasa, to komai zai tafi daidai.”
Birgediya janar Ka’a’ni ya kuma jinjina wa shahidai, yana mai kara da cewa; tafarkinsu zai cigaba da wanzuwa.
A lokacin yakin kwanaki 12 HKI ta rika watsa cewa ta kashe kwamandan na rundunar Kudus, lamarin da ya tabbata fargaganda ce.