Junbilat: ‘Yan Sahyoniya Suna Son Tarwatsa Kasar Syria

Fitaccen dan siyasar kasar Lebanon Walid Junbilat ya bayyana cewa, ‘yan sahayoniya suna son yin amfani da kungiyoyin da ake da su a Syria domin

Fitaccen dan siyasar kasar Lebanon Walid Junbilat ya bayyana cewa, ‘yan sahayoniya suna son yin amfani da kungiyoyin da ake da su a Syria domin tarwatsa hadin kan kasar.

Walid Junbilat  wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar “ al-takaddumil-Ishtiraki” ya ce zai ziyarci kasar Syria domin ganawa da mahukuntanta akan hatsarin dake tattare da tsoma bakin Isra’ila a cikin harkokin wannan yankin, musamman abinda yake faruwa a kudancin Syria.

Dan siyasar na kasar Lebanon  wanda ya yi taron manema labaru a jiya Lahadi ya yi gargadi akan yanayin da ake ciki a yankin “Jabalu-Duruz” da tsoma bakin HKI domin haddasa rashin tsaro a cikin wannan yankin.

Haka nan kuma ya yi tuni da yabo akan tarihin gwgawarmayar ‘yan Duruz’ da yadda su ka tabbatar da zaman Syria a matsayin kasa daya dunkulalliya a karkashin Sultan Pasha Atrash’ yana mai kara da cewa; ‘yan Duruz ba za su taba mika kai ga manufofin Benjamin Netanyahu ba.

Har ila yau ya yi ishara da yadda mafarkin ‘yan sahayoniya yake na fadada ikonsu a ko’ina ba tare da iyaka ba.

Dangane da kudancin Lebanon, Walid Junbilat ya ce abinda yake faruwa mamaya ce, yana mai kara da cewa; Zai ci gaba da adawa da duk wani sulhu da Isra’ila, matukar ba a kafa wa Falasdinawa kasarsu ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments