Search
Close this search box.

Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare Hare Kan Wasu Wurare A Cikin Kasar Siriya

Labaran da suke fitowa daga kasar Siriya sun bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hare hare da makamai masu linzami a kan wasu wurare

Labaran da suke fitowa daga kasar Siriya sun bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hare hare da makamai masu linzami a kan wasu wurare a birnin Damascus babban birnin kasar a jiya da dare.

Wasu kafafen yada labarai na kasar sun bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hare hare har sau uku a jiya da dare kan birnin Damascus.

Labarin ya kara da cewa garkuwan makamai masu linzami na sojojin kasar Siriya sun kakkabo da dama daga cikin makaman. Wata majiyar ta kara da cewa jiragen yakin sun kai hare haren ne a yankin kudu maso yammacin birnin ne.  Kuma hare haren sun yi sanadiyyar shahadar mutane 3 fararen hula, a yayinda wasu 9 suka ji Rauni. Sannan sun lalata wasu dukiyoyui a hare haren na jiya da dare.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon tace hare haren na HKI sun fada kan gidan wata yar an jarida mai suna Safaa Ahmad a unguwar Mezza na birnin Damascus. Banda haka jami’an kwana-kwana suna kokarin kashe gobarar da hare haren suka jawo.

Banda haka tashar talabijin ta gwamnatin kasar Siriya ta bayyana sanarwna cewa ma’aikacin ta guda ya rasa ransa ko yayi shahada a hare haren na jiragen yakin yahudawan,.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments