Iran Ta yi Tir Da Mataki Mai Harshen Damo Da MDD Ke Dauka

iran tayi da mataken da mambobin kasashen yamma a kwamitin tsaro na mdd ke dauka

Jakadan kasar iran a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya Gulam reza  darzi  yayi mummunan suka game a mataken da mambobin kasahen yamma a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ke dauka mai harshen damo da munafunci , kuma yayi kira ga Amurka ta gagauta kawo karshen yakin zalunci da take yi  da kuma dage takunkumin shiga da fito ta ruwa da ta sanya ba bisa ka’ida ba, idan da gake tana da niyar bin hanyar doflomasiya

Jakadan ya fadi hakan ne a lokacin da yake jawabi a gaban kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a jiya juma’a game da tashin tashina dake faruwa a tekun fasha da kuma mashigar Hurmuz, Gulam riza darzi ya jaddada cewa babban abin da ya jawo rikici a mashigar shi ne haramataccen yakin da kasar Amurka da isra’ila suka  kaddamar kan kasar iran  a ranar 13 ga watan yuli na shekara ta 2025 da kuma 28 ga watan fabarerun shekara ta 2026

Yace Amurka itace Azzaluma ba wadda aka zalumta ba, kuma yayi  tir da kisan gillan da aka yi wa jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah sayyid Ali khamena’I da kuma manyan jami’ai da masana ilimin kimiyar nukiliya na kasa iran

Haka zalika yace ya kamata kwamitin tsaro ya tunkarari Azzalumai da suka kai hari ne kai tsaye, ba wai wadanda aka zalumta  aka kai musu hari ba,  kuma ya yi kira ga kasar amurkaa da ta janye dukkan barazanar da take yi da suka sabama doka, ta mika wuta ga dokokin majalisar dinkin duniya

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted