Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya yi gargadin cewa rashin hukumta kasashen amurka da isra’ila kan yakin da ta kaddamar kan kasar iran da ya sabama doka, zai sanya alamar tambaya ga dokokin kasa da kasa kuma zai jefa tsaron ko wacce kasa cikin garari
A cikin wata kasida da ya wallafa araqchi ya bayyana cewa hari da amurka da isra’ila suka kai kan kasar iran ya sabama doka kuma a fili yake karya dokokin kasa da kasar ne da ta haramta yin amfani da karfi fiye da kima da kuma keta alfarma kasar iran
Yace harin da sojojin Amurka suka kaddamar kan kasar iran basu da sahale war kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kuma hakan ya sanya ake gani akwai yiyuwa fuskantar barazana da za ta iya tasowa a nan gaba, wanda ba zai iya zama dalili da za’a yi amfani da su wajen kare kai ba,
Haka zalika ya kara da cewa idan mai takama da karfi ya ba kan shi damar karya doka to ba iran ce kawai za ta kasance ragon layya ba, wadanda suka kirkiri dokokin kasa da kasa da hukumomi a majalisar dinkin duniya ma za su kasance ciki hadari, kuma ya yi gargadin cewa idan aka kasa hukumta mai kai hari to fa babu tsaron wata kasa da zai iya samun garanti