Dakarun IRGC a nan Iran sun bada sanarwan kakkafa makamai masu linzami dauke da ton biyu na abubuwan fashewa, wanda kuma yake iya kaiwa tazarar kilomita 1,500.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto mataimakin babban kwamandan dakarun IRGC na kasa, Manjo Janar Mostafa Izadi yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, duk wani harin da makiya zasu kaiwa kasar zai gamu da maida martani mai tsanani ba tare da jinkiri ba kuma ba tare da iyaka ba.
Tasnim ya kara da cewa, manjo Izadi ya bayyana haka ne a taron bankwana da shahidai 110 a nan Tehran wadanda aka gudanar da jana’izarsu a jami’ar Tehran.
Yace makiya suna tsammanin zasu kifar da tsarin da ke iko da JMI shekaru kimani 50 da suka gabata da sauki, su kifar da tsarin, su sauya zuwa tsarin da zai ci gaba da biyayya garesu, su kwace danyen man fetur na kasar kamar yanda suka yi a kasar Venezuela, su kuma kawo karshen dukkan kawayen Iran a yankin yammacin Asia. SU kuma kaskanta mutanen kasar Iran.
Janar Izadi ya ce, Sojojin Iran suna da karfi kuma suna da makamai wadanda suke iya daukar abubuwa masu fashewa har ton 2, sannan suna da karfin tafiya har zuwa tazarar kilomita akalla 1,500. Da wannan kuma zasu wargaza shirin makiya, su kuma bata anniyarsu ta kawo karshen gwamnatin kasar.
Yace IRGC zasu maida martani ba tare da jinkiri ba, kuma ba tare da la’akari da yanki ko kasaba, wannan sai ya sa makiya sun yi nadamar hare haren da suka kaiwa kasar.
Kafin haka dai Jagoran Juyin Juya halin musulunci Aya. Sayyid Mujtaba Aliyul Khaminaei ya bada umurni ga sojojin kasar su shirya maida martani mai tsanani mai kuma sanya nadama kan makiya ba tare da lura da kan iyakokin kasashe ba, sannan sun sharya kare kasar daga makiya tare da duk karfin da suke da shi.