Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa amfani da karfi wanda manya manyan kasashen duniya suke yi kan wasu kasasa ba tare da amincewar MDD ba, ba zai takaita ga kasar da aka kaiwa farmaki ko aka mamaye ba, matsalar, idan ba’a magance ta ba, to zata zama barazana ga sauran kasashe duniya, banda haka hatta kundin dokokin MDD yana cikin hatsari.
Tashar talabijan ta presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar Kyodo News wacce ta buga rubutun ministan, ya ce hare haren da Amurka da HKI suka kai kan kasar Iran ya sabawa dokokin MDD na amfani da karfi kan wata kasa. Yace rashin daukar mataki kan Amurka da HKI yana da mummunan sakamako, don ba wai kawai yana iya bata al-amura a yankin kadai ba, sai dai, sai dai yana iya kaiwa ga sanya ayar tambaya kan dokokin MDD. Da kuma ikonta a kan daidata al-amura a duniya.
Saboda idan an bar wata kasa mai karfi ta take dokokin kasa da kasa kamarhaka, ba kasar Iran ce kadai abin zai shafa ba, sai dai al-amarin yana barazana ne ga dokokin kasada kasa, yana kuma saka ayar tambaya a kan halaccin ikon MDD a kan kasashen duniya.
Daga karshe ministan ya bayyana cewa, dole ne Amurka ta kawo karshen yaki a kan kasar Iran, ta muntunta diyaucin kasar ta biya diyyar barnan da ta yi mata ta kuma koma kan mutunta dokokin kasa da kasa.