Tare da umurnin jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Aya. Sayyid Mujtaba Khaminaei, shugaban ofishe mai kula da ayyukan Imam Khaminaei a nan Tehran ya bada sanarwan kafa Kwamiti wanda zai shirya juyayin shahadar Imam Khaminaei (a) a cikin watan Esfan mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ofishin Imam Shahid yana cewa kwamitoin ya Kunshi mataimakin shugaban kasa na farko Mohammad Reza Aref; Hojjatoleslam Ahmad Marvi, mai kula da haramin Imam Riza (a) mai tsarki,; Hossein Taeb, shugaban rundunar Basij sojojin sa kai na kasar, Gholam Ali Haddad-Adel, mai bawa jagora shawara Ali Akbar Haji-Akbari, shugaban kwamitin limaman masallatan Jumma’a na kasa. Da kuma magajinn garin Tehran Alireza Zakani.
Wannan kwamitin ne zai kula da dukkan shirye shiryen juyayin cika shekara guda da shahadar Imam Shahid(q) a ciki da wajen nkasar.