Sojojin ruwa na kasar Iran sun bada labarin kakkabo jirgin yakin kasar Amurka samfurin US MQ-1 wanda ake sarrafa shi daga nesa ko Drons tare da amfani da tsarin garkuwan sararin samaniyar kasar mai inganci kuma na zamani, a kan garin Kuhestak a lardin Hurmuz. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto sojojin ruwan na fadar cewa, sun kakkabo jirgin a kusa da garin Sirik na lardin Hurmuzgan a bakin ruwan tekun farisa.
US MQ-1 dai jirgin yaki wanda yake dauke da makamai yake kuma aikin leken asiri a lokaci guda. Kuma kamfani General Atomics na kasar Amurka mallakin US Air Force ne suka kera shi.
Amurka ta sha amfani da irin wadannan jirage a kasashe daban daban a kasashen Asiya ta yamma da wasu yankuna .
Amma sojojin JMI sun sha kakkabo samfurin MQ-9 wanda ya fishi karfi a yakin da Amurka da HKI suka dorawa JMI tun watan yolin shekara ta 2025, inda ta kakkabo fiye da 50 daga cikinsu. Sai ta sake komawa kan MQ-1 don ta ci gaba keta hurumin JMI, duk da cewa sun san cewa JMI tana da karfin kakkabosu.