Sojojin Isra’ila Sun Kashe Akalla Yara Falasdinawa 245 A Gaza

majalisar dinkin duniya ta ce sojojin isra'il sun kashe yara falasdinawa 245 gabar yammacin kogin jodan

Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa sojojin isra’ila sun kashe akalla yara faladinawa guda 245 a gabar yammacin kogin jodan da aka mamaye tun daga ranar 7 ga watan oktoban shekar ta 2023 lokacin da ta kaddamar da yakin  kare dangi  kan alummar gaza

Yayi wannan bayanin ne a jiya juma’a inda ya kara da cewa wadanda abin ya shafa har da kananan yara 41  wanda suka rasa rayukansu sakamakon harbe harbe da duwatsu. yace kisan yara kanana abin yin tir ne, kashe yaro don ya dauki dutse ko ya jefesu abu ne mai muni matuka.

Hukumar ta jaddada cewa dokokin kasa da kasa sun bukaci duk wani amfani da karfi idan ya zama wajibi dole ne yayi daidai da barazanar da aka fuskanta, ya kara da cewa dole na a dauki alhakin keta dokokin kasa da kasa ga duk wanda ya aikata haka

Rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar ya nuna cewa kimanin falasdinawa 1143 ciki har da yara 250 ne aka kashe a gabar yammacin kogin jodan kuma ya hada da adadin faladinawa da yan share wuri zauna suka kashe a yankin da suka hada da Khalil , ramalla, Nablus. jenin da kuma al-bireh

A ranar 10 ga watan nuwamba  sojojin isra’ila sun harbe wani bafalasdine dan shekaru 14 kuma suka jikkata wasu matasan gud biyu a wani samame da suka kai a kauyen burqa dake gabar yammacin kogin jodan da aka mamaye

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted