Rahotanni sun bayyana cewa Attajirin dan kasuwa kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, aliko dan gote ya bayyana shirinsa na zuba jari a fannin samar da wutar lantarki domin magance matsalar karancin wutar da ke kawo cikas ga masana’antu da bunkasar tattalin arziƙin Nijeriya da sauran kasashen Afirka. Ya ce shirin na daga cikin manufofin kamfaninsa na Vision 2030, kuma yana nazarin samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 10,000 a faɗin Afirka, ciki har da yiwuwar Nijeriya.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki a masana’antun kirkira daga Arewacin Nijeriya, ciki har da ƴan jarida, da masu shirya fina-finai da masu amfani da kafafen sada zumunta, a Matatar Dangote da ke Legas. Ya ce kamfaninsa na shirin kara yawan jarin da zai zuba a Afirka daga dala biliyan 50 zuwa kusan dala biliyan 70, domin fadada ayyukan masana’antu, da samar da ayyukan yi da karfafa tattalin arzikin nahiyar.
haka zalia ya ce kamfanonin rukunin Dangote a halin yanzu suna samar da wutar lantarki mai karfin kusan megawatt 1,500 domin gudanar da ayyukansu, amma ana sa ran zai karu zuwa tsakanin megawatt 4,500 da 5,000 kafin kammala shirin Vision 2030. Ya jaddada cewa wannan karfin na cikin gida ne domin amfanin kamfanoninsa, yayin da shirin samar da megawatt 10,000 a faɗin Afirka kuma yake a wani mataki ne na daban da zai iya shafar samar da wutar ga sauran masu amfani.