Darzi: Idan Amurka Da Gaske Take Ta Daukewa Iran Takunkuman

Jakadan kasar Iran a MDD ya bayyana cewa, idan da gaske Amurka tana bukatar warware matsalolinta da JMI ta hanyar Diblomasiyya, to dole ne ta

Jakadan kasar Iran a MDD ya bayyana cewa, idan da gaske Amurka tana bukatar warware matsalolinta da JMI ta hanyar Diblomasiyya, to dole ne ta dauke dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa JMI ta kawo karshen killacewar da suke wa kasar ta ruwa da sama da kasa ba tare da wani sharadi ba. Ta mutunta diyaucin JMI ta kiyaye hakkokinta sannan daga karshe ta dauki alkawali ba zata sake maimata hare haren da ta kaiwa kasar a bay aba, sannan ta biya diyyar dukkan asarorin da ta jawowa kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na jmi ya nakalto Gholam Hussain Darzi jakadan JMI a MDD yana fadar haka a taron kwamitin tsaro na majalisar a birnin NewYork a jiya Jumma’a 13ga watan Nuwamban shekara ta 2026. Inda kwamitin ya sake yin nazari kan yanda al-amura suke gudana a yankin gabas ta tsakiya.

Darzi ya kara da cewa, har yanzun JMI bata rufe kofar doblomasiyya ba, sannan a cikin shekaru biyu da suka gabata ta sha haduwa da Jami’an gwamnatin Amurka don tattaunawa dakuma warware sabanin da ke tsakanin kasashen biyu. Ya ce, amma a dukkanin wadan nan tarurruka gwamnatin Amurka daga karshe tana amfani da karfi don don cimma manufofinta kan kasar Iran amma ta kasa yin hakan. Sannan da alamun har yanzun tana kokarin ganin ta cimma munanan manufofinta a kasar.

Babban jami’an diblomasiyyar JMI a wannan cibiyar kasa da kasa, ya kammala da cewa Iran tana shakkan Amurka a duk abinda ta yi, saboda ta rika ta sanya rashin amince a da kuma cika alkawali a cikin dukkan alkawulanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted