Jiragen fasinja na kamfanin jiragen gwamnatin kasar Iraki sun dawo da zirga zirgar tsakanin kasar da JMI bayan da aka dakatar da hakan, a lokacin da gwamnatin Amurka ta kakabawa jirage shiga ko fita daga kasar Iran daga ciki haar da jiragen Iran kanta.
Shafin yanar gizo na labarai Arabnews na kasar Saudia ya bada labarin cewa bayan dakatar da zirga zirgar na kwanaki biyu firay ministan kasar Iraki Ali Al-Zaidi ya ce ya sami izini daga gwamnatin kasar Amurka na fittar da kasar Iraki daga haramcin da ta yiwa JMI.
Kamfanin dillancin labaran na gwamnatin kasar Iraki INA ya ce an sake dawo da zirga zirgan tun jiya litinin da yamma daga birnin Najaf mai tsarki. Gwamnatin kasar ta Iraki ta dakatar da zirga zirgan ne don kaucewa barazanar Amurka na kakabawa duk wata kasa da ta sabwa umurninta. Kamar yanda ma’aikatar kudi ta Amurka ta bayyana.
Kafin haka dai Jikadan kasar Iraki a nan Tehran Yasser Abduzzahra Hajjai ya bayyana cewa, za’a bude tashar jiragen sama na Najaf mai tsarki ba da dadewa ba.
Yace kamfanoni masu gudanar da ayyuka a tashoshin jiragen sama,kuma na kasashen waje, ne suka ce ba zasu yi wata khidima da duk jirgin da zai zo ko ya tafi kasar Iran ba don suna tsoron kasar Amurka zata cutar da su.
Banda haka a wani bangare kuma JMI ta shigar da kara a hukumar zirga zirgan jiragen sama ta kasa da kasa International Civil Aviation Organization (ICAO) don daukar matakin da ya dace kan Amurka dangane da haramta khidima wa jiragen kasar Iran ko masu zuwa kasar.
Shugaban hukumar zirga zirgan jiragen sama na Iran Abuzar Shiroudi ya bayyana cewa hukumarsa tana aiki tukuru da wadanda al-amarin ya shafa don dauke haramcin.
A ranar 8 ga watan satumban da muke ciki ne ma’aikatar baitul Amurka ta bada sanarwan cewa, duk wani kamfanin khidima da yayiwa kamfanonin jiragen sama na kasar Iran 27 to shima za’a dora masa takunkumin tattalin arziki a matsaki na biyu.
A halin yanzu dai gwamnatin kasar ta Iraki ta tabbatar da cewa Amurka ta fidda kamfanonin khidima da suke kasar Iraki daga wannan haramcin.