Rahotanni daga kasar Iraqi sun nuna cewa kasar Italiya ta sanar da janye bataliyar karshe na sojojinta daga kasar iraki wanda ya kawo karshen zamansu a kasar iraki tsawon shekaru 12 da suka gabata kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta bayyana
Wannan ci gaba ya zo ne a yau talata bayan da gwamnatin Roma ta sanar da janye sauran sojojinta dake kasar Iraqi da suka fara ficewa a watan maris din shekara ta 2026, bayan hare haren da aka kai a cikin dare kan sansaninsu dake yankin kurdawa na kasar Iraqi
Sojojin italiya wani bangare ne gammayar sojojin da amurka ta jagoranta domin yaki da kungiyar takfir ta Daesh, da kuma ayyukan da dakarun tsaro na nato suka taka a kasar, da suka shafi bayar da shawarwari da kuma bada karfin guiwa ba tare da sun shiga filin da ga ba.
Ana shi bangaren fira ministan iraki Ali al-zaidi ya bayyana cewa ranar 30 ga watan satumba ne aka tsare dakarun hadin guiwa da Amurka ke jagoranta za su karasa ficewa baki daya daga kasar iran .tuni sojojin Amurka suka fice daga mafiyawancin sansanoninsu dake fadin kasar a shekara da ta wuce, sai dai za su ci gaba da kasancewa a wani bangaren a yankin kurdawa.