Iran: Idan Ba’a Tabbatar Da Tsaron Iran Ba To Ba Wanda Zai Samu Tsaro

iran tace idan dai iran bata da tsaro kuma ba za ta sayar da manta ba,to babu wanda zai samu tsaro

shugaban majalisar dokokin kasar iran Mohammad Baqeer qalibaf yayi gargadin cewa duk kasar da ta bari aka yi amfani da ita wajen kawo cikas ga siyar da manfetur din iran ko kuma jefa ta cikin matsalar tsaro to za ta biya farashi mai tsada

Yace ya kamata Amurka da sauran kasashen duniya su sani cewa kamar yadda muka fadi a baya, a duk yankin da ba zamu iya sayar da man fetur dinmu ba, to kuma babu wanda zai sayar da nasa, idan kuma babu lamuni akan tsaro da zaman lafiyarmu to babu wani muhimmin wuri da zai kasance cikin tsaro

Haka zalika ya kara da cewa iran za ta mayar da martani kan duk wani mataki da Amurka za ta dauka na kakaba takunkumi hana zirga zirga jiragen ruwa, ko rufe sararin samaniyar iran  ko kuma matsa lamba kan hanyoyin samar da kayayyaki masu muhimmanci ga tattalin arzikinta,

inda ya kwatanta hakan da irin yadda aka karyar kawanyar da aka yi wa birnin Abadan dake kudu maso yammacin iran, a lokacin kallafafen yaki da tsohon shugaban kasar iraki ya kakabawa kasar iran a shekara ta 1980

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted