Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya mayarwa shuwagabannin fadar White House kan cewa, takunkuman kudade, ko na tashin jiragen sama da sauransu, ba zasu sa mutanen Iran su jada baya kan matsayinsu na neman hakkinsu, da tunkude zaluncin azzalumai ba.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a yau Talata a majalisar dokokin kasar ya kuma kara da cewa, duk wani hari a kan JMI zai jawo nadama ga Amurka.
Ya kuma kara da cewa mutanen suke ta tarihin bada shidai a kallafeffen yaki da farko na tsawon shekaru 8, da na biyu na kwanaki 12 da kuma na uku na tsawon kwanaki 40, ba wanda ya isa ya tsoratasu ko yayi masu barazana da yaki.
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran ya kara da cewa, idan Amurka ta sake kuskuren fadawa Iran da yaki, zata gamu da maida martani mai tsanani fiye da wanda ta sha a baya. Yace kalaman shugaban kasar Amurka a babban zauren MDD a ranar 23 ga watan Satumba ya nuna cewa har yanzun basu sauya halayencu ba. Amma jawabimmu shi ne kamar yanda ake cewa ka juya mu kuma mujujjuya.