Farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya sun kara tashi sama kwanaki biyu a jere sanadiyyar rufe mashigar ruwa ta Hurmuz wanda JMI ta yi watanni kimani 6 da suka gabata.
Shafin yanar gizo na Arabnews ya bayyaa cewa farashin danyen man fetur na Brent ya tashi da kashi 1.6% zuwa $106.99 sai kuma na Texas ta yamma kuma ya tashi da $.1.4 zuwa $94.
Labarin ya kara da cewa, farashin man wanda za’a isar a cikin watan Nuwamba mai kuma ya kama dalar $106.99 a yau talata bayan karin da ya samu a jiya Litinin sannan na watan decemba kuma an saida shi kan dalar $99.51 kan ko wacce ganga. A jiya dai wato ranar Litinin ko wanne daga cikin nau\oin man sun karu da dalar Amurka guda.
Wannan yana faruwa saboda kin amincewa da shawarorin da Iran ta gabatar da bude mashigar idan Amurka ta aiwatar da sharuddanta guda 7 a cikin mako guda.