Rahotanni daga kasar labanon sun ce shugaban majalisar dokokin kasar labanon Nabih Berri ya fadi cewa kasar labanon tana da hakkin daukar matakin doka kan isra’ila game da ci gaba da hare haren da ta kai wa a kudancin kasar labanon , kana yayi kira da a kara matsin lamba don kawo karshen mataken soji da isra’ila ke dauka
Haka zalika ya kara da cew kasar labanon na da hakkin gurfanar da isara’ila a gaban shari’a kan laifukan yaki da ta aikata kan alummar labanon, kuma ya fadi hakan ne a yau talata a lokacin da ya karbi bakunci wani dan majalisar Amurka Darin lahood da kuma jakadan amurka a labanon da ya mara masa baya
Shugaban majalisar yace Amurka da shugabanta Donald trump su ne kawai suke da karfin da za su iya yin matsin lamba kan isra’ila da kuma gamsar da ita ta dakatar da ci gaba da mamaya da hare haren da take kai wa a kasar labanon.
Duk da yarjejeniyar da aka cimma, amma har yanzu isra’ila na ci gaba da daukar matakin soji kan alummar labanon ,inda gwamnatin labanon ta ce hare haren isra’ila sun yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 4386 tare kuma da jikkata mutane 12407 da kuma tilastawa sama da miliyan daya barin gidajensu tun a watan maris.