Shugaban Ghana Ya Fadi Dalilan Kin Karbar Shirin Lafiyar Amurka

shugaban kasar Ghana ya bayyana dalilan sa na rashin amincewa da shirin lafiya da Amurka ta gabatar

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya bayyana wasu daga cikin dalilan da suka sa kasar ta janye daga Shirin Kiwon Lafiya da Amurka ta gabatar ma ta kamar dai sauran kasashen duniya masu tasowa, inda ya bayyana shirin a matsayin kaskanci.

Shugaban John Mahama wanda ke gabatar da jawabi a wata tattaunawa da ta gudana a gefen Taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York, ya ce bayan nazari, ya fahinci cewa amincewa da wannan shiri, zai iya zama babbar barazana ga makomar kasar Ghana.

A karkashin wannan shiri dai, Amurka ta tsara bai wa Ghana dala miliyan Dari, to amma dole sai mahukuntan birnin Accra sun tattara dukkan bayanan kiwon lafiya na al’ummar kasar sun mika wa Amurka, kuma a game da wannan sharadi ne aka samu sabani tsakanin bangarorin biyu.

Amurka dai ta bayyana shirin a matsayin wanda zai maye gurbin tallafin kudade da take bai wa kasashe masu tasowa karkashin hukumar nan ta USAID, kuma tuni wasu kasashen Afirka da dama suka amince da shi duk da irin adawar da yake fuskanta daga wasu masu fafutuka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted