Aragchi: Babu Sauyi A Matsayin Na Shirin Makamashin Nukliya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran bata sauya matsayinta ko kadan dangane da hakkintana tache makamashin Uranium ba, sannan a

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran bata sauya matsayinta ko kadan dangane da hakkintana tache makamashin Uranium ba, sannan a yau talata ce ake saran amsar gwamnatin kasar Amurka dangane da shirin da Iran ta gabatar na bude mashigar ruwa ta Hurmuz daga hannun gwamnatin Qatar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka jim kadan kafin ya kama hanyarsa ta komawa gida dag birnin New York a yau Talata.

Ministan ya kara da cewa, a tattaunawarsa ta karshe da masu shiga tsakani na kasar Qatar, sun fada masa cewa akwai yiyuwar amincewar Amurka da sharudda guda 7 da Iran ta aika mata. Kafin haka dai a cikin Jama’a a a gaban yan Jaridu shugaban Amurka yace ba zai amince da shirin kasar Iran na bude mashigar ruwa ta Hurmuz a cikin kwanaki 7 ba. Amma muna jiran jawabin a rubuce ko kuma ta inda muka saba samunsu.

Yace abinda muke jira a halin yanzu shi ne cika sharudda guda 7 wadanda muka gabatar don bude mashigar ruwar a cikin mako guda. Muna kuma jiran amsar Amurka a yau talata.

Dangane da shirin makamashin Nukliya na kasar Iran kuma Aragchi yace, iran ba zata sauya matsayinta na hakkin tache makamashin uranium ba ko kadan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted