Babban Hafsan Sojin Iran: Za A Mayar Da Martani Ga Barazana

Babban Hafsan Sojojin Iran ya bayyana cewa: Sojojin Iran da ‘yan gwagwarmaya za su mayar da martani mai tsanani ga duk wata barazana Babban Hafsan

Babban Hafsan Sojojin Iran ya bayyana cewa: Sojojin Iran da ‘yan gwagwarmaya za su mayar da martani mai tsanani ga duk wata barazana

Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran Manjo Janar Abdur-rahim Mousavi ya bayyana cewa: Sojojin Iran, tare da mayakan sa- kai da kuma mujahidai masu kishin Musulunci, sun shirya tsaf don mayar da martani mai tsanani ga duk wata barazana da al’ummar Musulmi ke fuskanta.

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Manjo Janar Abdur-Rahim Mousavi, Babban Hafsan Sojojin Kasa kuma Kwamandan Hedikwatar Tsakiya ta Khatam al-Anbiya, ya fitar da sako kan cika shekaru biyu da shahadar Sayyid Hassan Nasrallah, tsohon Babban Sakataren kungiyar Hizbullah. Da yake tsokaci kan yunƙurin maƙiya ‘yan Sahayoniyya da Amurka na raunana ƙungiyar gwagwarmayar ta Hizbullahi, ya ce: “Maƙiya sun ruɗa kansu suna tsammanin cewa rashin Jagoran ‘yan gwagwarmaya zai haifar da rugujewar ginshiƙan kungiyar gwagwarmayar, lamarin da ya rusa lissafin maƙiya ya sake nuna gazawarsu.”

Ya ƙara da cewa: Kungiyar gwagwarmaya ba wai kawai ba ta raunana ba, har ma ta cimma haɗin kai mai mahimmanci – a bayyane da kuma a ɓoye.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted