Hamas Tayi Kira Ga Musulmi Da Su Kare Masallacin Ibrahimi

kungiyar Hamas ta yi kira ga dukkan musulmi da su kare masallacin ibrahimi da isra'ila ke kokrin mamayewa

Kungiyar gwagwarmar musulunci ta Hamas ta yi kira ga kasashen larabawa da na musulmi da su tashi tsaye wajen kare wurare masu tsarki na musulunci  bayan da ministan isra’ila Itamar Ben Gvir tare da daruruwan yahudawa yan share wuri zauna suka kutsa kai a masallacin Ibarahimi a Khalil, inda ta bayyana matakin a matsayin wani makirci na mayar da wuraren na yahudawa

Abdel Rahman shaddid daya daga cikin jagororin kungiyar Hamas yace Ben Gvir ya kutsa kai cikin masallacin ibrahimi ne tare da wasu yahudawa yan share wuri zauna da kuma wasu malaman yahudawa, wanda wannan keta alfarmar masallacin da kuma miliyoyin musulmi ne a duniya

Haka zalika Shahid yayi kira ga falasdinawa a gabar yammacin kogin jodan  musamman mazauna yankin Khalil da su mike domin kare masallacin, kuma su ci gaba da kasancewa a wajen, kana yayi kira ga kasashen larabawa da na musulmi da su mike domin kare wurare masu tsarki na musulunci

Ana sa bangaren ministan awqaf da alamuran addini na yankin falasdinu yayi tir da matakin, yace  hana musulmi gudanar da ibada da yin sallah da sauran ayyukan addini a masallacin da kuma hana kiran sallah ya sabama hakkin gudanar da ayyukan addini ba tare da tsangwama ba, haka zalika ma’aikatar ta bayyana masallacin a matsayin babbar kadarar waqafi ta musulunci,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted