Rahotanni daga iran sun bayyana cewa jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah mujtaba hussain kahamina’I ya sanar da sunayen sabben manyan kwamandoji guda 6 na rundunar sojin kasar ciki har da kwamandan dakarun kare juyin musulunci na kasar iran
A cikin sakon da jagoran ya aike da shi a jiya litinin ya bayyana Majo Janaral Ali Abdullahi a matsayin sabon kwamandan hafsan sojojin kasar, sai kuma birgediya Janar Kiomars Haidari a matsayin mataimakinsa, sai kuma Majo Janarar Ahmad Vahidi shi kuma an kara marasa mukami zuwa matsayin major janaral a matsayin babban kwamandan dakarun kare juyin musulunci na kasar iran, sai kuma major janaral Mostapha Izadi a matsayin mataimakinsa.
haka zalika Reyal Admiral Ali Ozamae an nada shi a matsayin kwamanda hafsoshin sojin ruwa na dakarun kare juyin musulunci sai kuma hujjatul Islam Hossain Taeb a matsayin shugaban hukumar dakarun sa kai na kasa wato Basij.
A daya bangaren kuma jagoran ya nada major Janaral Aliu Abdullahi a matsayin kwamandan hafsan hafsoshin sojojin kasar , bayan shahadar wanda ya gabaceshi major Ganaral Abdulrahim musawi a harin da Amurka da Isra’ila suka kawo.
Ayatullah sayyid mujtaba Hussain Khamina’I ya ce an yi wannan nadin ne saboda tunawa da shahadar musavi mai girma da daraja a hannun makiya isra’ila da Amurka da kuma nuna jinjina ga ayyukan da abdullahi yayi da kuma kwarewarsa.