Jagora: Iran Tana Fuskantar  Makiya Na Waje Kafirai Da Munafikai

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; al’ummar Iran tana fuskantar makiya kafirai da munafikai, amma kasar ba

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; al’ummar Iran tana fuskantar makiya kafirai da munafikai, amma kasar ba ta da matsala da sauran al’ummun duniya.

Har ila yau jagoran ya ce, alkur’ani mai girma yana kunshe da hanyoyin da ya kamata a yi mu’amala da dukkanin wadannan makiyan, da kuma lokacin da ya kamata a yi Magana da su, ko kuma lokacin da ya kamata a zare musu takobi.” Dukkanin wadannan bayanan suna cikin al’kur’ani mai girma.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron karatun alkur’ani mai girma, a jiya Lahadi da dare, ya yi ishara da cutukan ruhi da su ka addabi bil’adama a wannan  zamanin da su ka hada hassada, rowa,mummunan zato, ganda da son kai, da kuma fifita manufa ta kashin kai akan ta al’umma, tare da bayyana cewa, a cikin alkur’ani mai girma da akwai magungunan dukkanin wadannan cutukan.

Jagoran juyin musuluncin ya kuma ce, a bisa mahanga ta musulunci abu na biyu mai muhimmanci bayan tauhidi da ilimi da kyautata alaka da Allah, shi ne shimfida adalci a cikin al’ummar musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments