Isra’ila ta kai hare-hare ta sama a kudanci da gabashin Lebanon, inda ta sake karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
Sojojin Isra’ila sun kai hare-hare daban-daban kan garin al-Manara a kwarin Bekaa da gundumar Jezzine a kudancin Lebanon.
A cewar rundunar sojin Isra’ila, hare-haren sun farmawa wuraren da take ikirarin cewa mallakar kungiyar Hezbollah da Hamas ne.
Wani mai magana da yawun rundunar ya bayyana a baya cewa an shirya kai hare-haren sama kan “kayayyakin more rayuwa na soja” a kauyukan Hammara da Ain el-Tineh a kwarin Bekaa, gabashin Lebanon, da kuma a Kfar Hatta da Annan a kudu.
Tashar Al Jazeera, ta ambato majiyar Hamas, ta tabbatar da cewa hukumomin mamayar suna kirkirar hujjoji na karya don tabbatar da ci gaba da kai hare-haren da suke yi wa al’ummar Falasdinawa a Gaza da Lebanon.
Wannan majiyar ta kara da cewa ikirarin Isra’ila game da kasancewar kayayyakin more rayuwa na Hizbollah a Lebanon ba shi da tushe kuma bashi da hujja kwai don dai halatta ci gaba da kai hare-hare.
Majiyoyin yankin sun ba da rahoton jin karar fashewar abubuwa kusa da sansanin ‘yan gudun hijira na Ain al-Hilweh, kusa da birnin Sidon da ke kudancin Lebanon, bayan wani hari da Isra’ila ta kai a yankin.
Rundunar Sojan Sama ta Isra’ila ta kuma kai hare-hare sau biyu a sansanin Ain al-Hilweh. An ji karar fashewar abubuwa a yankin da ke kewaye.
Har yanzu ba a fitar da wani karin bayani game da yiwuwar asarar rayuka ko asarar dukiya ba, kuma majiyoyin gida da na soja sun nuna cewa ana ci gaba da tantancewa.