Isra’ila Ta Kai Jerin Hare-hare A Kasar Lebanon

A jiya Litinin da marece jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai jerin hare-hare a cikin kasar Lebanon a wuraren da su ka kira na

A jiya Litinin da marece jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai jerin hare-hare a cikin kasar Lebanon a wuraren da su ka kira na kungiyoyin Hizbullah da Hamas.

Rahotanni daga kasar ta Lebanon sun ambaci cewa wuraren da hare-haren na ‘yan sahayoniya su ka shafa sun hada kauyen Anan dake gundumar Jazzin akudancin Lebanon, da kuma garuruwan Ainit-tinah da Manarah a yankin Bika  a gabashin Lebanon.

Tun da fari, mai Magana da yawun sojojin Lebanon ya kira yi mazauna kauyuka 4 dake gabashin Lebanon din da su fice daga cikinsu gabanin kai hare-haren.

Kakakin sojojin sahayoniyar ya kuma ce; za su kai hare-haren ne akan cibiyoyin Hizbullah da Hamas a garuruwan Himarah, da Ainit-tina da Bika dake gabashin kasar Lebanon, sai kuma Kafar-Hatta da Anan a kudancin kasar.

Tun da aka tsayar da wutar yaki a 2024 Haramtacciyar Kasar Isra’ila ba ta daina kai hare-hare ba, da hakan yake a matsayin ci gaba da keta yarjejeniyar.

Lebanon na fuskantar matsin lamba akan cewa dole ta kwance damarar yakin kungiyar Hizbullah.

Kungiyar ta Hizbullah ta bakin babban magatakardarta Sheikh Na’im Kassim ta ce, ba za ta mika wa abokan makamanta ba.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted